BORIN KUNYA: Gwamnatin Kogi ta ce ba ita ta ɓoye naira biliyan 19.3 a Bankin Sterling ba

Gwamnantin Jihar Kogi ta bayyana cewa danganta ta da EFCC ta yi da kimshe naira biliyan 19.33 a Bankin Sterling, ƙarya ce, sharri ne da tuggun ɓata wa Gwamna Yahaya Bello suna.

A kan haka ne a cikin wata sanarwar da Kwamishinan Laɗa Labarai na Jihar Kogi, Kingsley Fanwo ya ce idan EFCC ba ta bayar da haƙuri ba da gaggawa, to za su dauki matakin maka EFCC ɗin kotu, domin biyan diyyar ɓata sunan Gwamnatin Jihar suna.

Kwamishina Fanwo ya ce, “ba mu san yadda aka yi EFCC ta ƙirƙiri ƙarya ta kantara wa Jihar Kogi.

“Sannan kuma ba mu san inda EFCC ta rakito wani lambar asusun ajiyar kuɗi mai lamba 0073572696 ba, domin ba asusun ajiyar Gwamnatin Kogi ba ne.”

Gwamnatin Yahaya Bello ta yi wa EFCC raddi kan bankaɗo naira biliyan 19.2

Kwana ɗaya bayan da EFCC ta fallasa cewa Bankin Sterling ya maida wa CBN naira biliyan 19.2 waɗanda gwamnatin jihar Kogi ta ɓoye, ta ƙi biyan ma’aikatan jihar, Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar Kogi ya maida raddi, ya ce su na da hujjar cewa iƙirarin da EFCC ta yi ba gaskiya ba ne.

Sai dai kuma bai bayyana wata cikakkiyar hujja ba, amma ya ce za su tsaya filla-filla gaskiyar maganar, domin su tabbatar wa duniya cewa zancen EFCC ba gaskiya ba ne.

EFCC dai ta bada adadin kuɗaɗen da Sterling Bank ya maida wa CBN cewa Naira 19,333,333,333.36 ne cif-da-cif.

Ranar Juma’a ce wannan jarida ta buga labarin cewa EFCC da Sterling Bank sun maida naira biliyan 19.23 a CBN, kuɗaɗen albashin da Gwamna Yahaya Bello ya ɓoye bai biya ma’aikata ba.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar cewa Bankin Sterling ya maida masa zunzurutun naira biliyan 19.3, da wadda EFCC ta bankaɗo cewa kuɗaɗen tallafin biyan ma’aikata albashi ne da Gwamnatin Tarayya ta ba Jihar Kogi, amma Gwamna Yahaya Bello ya ɓoye kuɗaɗen a Sterling Bank.

Cikin wata sanarwa da Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar a ranar Juma’a, ya ce CBN ya tabbatar da karɓar kuɗaɗen daga Sterling Bank.

Tun da farko dai jihar Kogi ƙarƙashin Yahaya Bello ta kasance tsawon watanni ba ta biya albashi ba.

Sai gwamnatin tarayya ta bayar da kuɗaɗen rufin asirin da za a biya ma’aikatan jihar albashi.

Maimakon Gwamna ya sa a biya, sai ya sa aka ɓoye kuɗaɗen a wani asusun da a kullum za a riƙa samun kuɗin ruwa, maimakon a ajiye cikin asusun albashin ma’aikata.

Yayin da EFCC ta gano inda Yahaya Bello ya ɓoye kuɗaɗen, ta garzaya Babbar Kotun Tarayya a Legas, inda ta nemi a ba ta damar riƙe kuɗaɗen.

A ranar 31 Ga Agusta ne Mai Shari’a TJ Ringim ya kulle asusun, ya hana Gwamnatin Kogi amfani da kuɗin.

Daga baya EFCC ta nemi kotu ta buɗe asusun, tare da umartar Sterling Bank ya maida kuɗaɗen Asusun Gwamnantin Tarayya a CBN.

Cikin watan Oktoba ne Mai Shari’a Chukwujekwu Aneke na Babbar Kotun Tarayya a Legas ya bayar da umurnin.

Yahaya Bello wanda ke haƙilon neman takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin APC, ya kasance a cikin wannan shekara ya na ta bindiga da kuɗaɗen jihar wajen yi masa kamfen, tun ma kafin lokacin kamfen ɗin ya gabato.

A yanzu haka ɗimbin ‘yan fim ɗin Kannywood sun karkata wajen shirya masa wakokin kamfen birjik, waɗanda ake kashe makudan miliyoyin kuɗaɗe wajen shirya su.