Tir da kisan mutum 34 da aka yi a kauyen Madami, jihar Kaduna – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai yayi alhinin kisan mutum 34 da ‘yan bindiga suka yi wa wasu mazauna kauyen Madami dake karamar hukumar Kaura jihar Kaduna.

Kwamishinan Tsaron Jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamna El-Rufai ya ya aika da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan hari sannan ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ta gaggauta kai kayan agaji ga wadanda abin ya shafa.

Akalla mutum 34 ne suka rasa rayukan su a harin wanda aka kai wannan kauye.

Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Mohammed Jalige ya bayyana cewa yan sanda sun damke wasu masu garkuwa da mutane biyar a Zaria.

Jalige ya kara da cewa yan sandan sun kashe wani daya daga cikin yan bindiga.