Muhimman batutuwan da Gwamnoni da Sarakunan Arewa suka tattauna a Kaduna

Daga Ubaidullah Yahaya Kara

Gwamnonin Arewa sun nemi Sojoji da su mamaye jihohin dake fama da matsalolin tsaro domin yaki da matsalar gadan-gadan.
Haka Gwamnonin sun yi watsi da bukatar Gwamnonin kudancin Najeriya da sukace dole sai shugabancin kasa ya koma Kudancin Najeriya 2023.
Ga dai wasu muhimman abubuwa da taron ya mayar da hankali a kai: kamar yadda kafar yada labarai ta BBC hausa ta ruwaito.

Muhimman batutuwan da Gwamnoni da Sarakunan Arewa suka tattauna a Kaduna
Mutane 30 sun mutu a wani sabon harin mai kan uwa-da-wabi a Kaduna

Kungiyar ta sake nazari kan batun sha’anin tsaro na baya-bayan nan daga yankin, ta kuma gano cewa akwai bukatar hada kai da kara kokari tsakanin gwamnatin Tarayya da jihohin arewacin kasar, a yayin da ta kuma yi duba kan matakan baya-bayan nan da aka dauka.

Taron ya kuma nuna damuwa kan matsalolin da jami’an tsaro ke fuskanta sannan ya nemi rundunar soji ta kaddamar da wani aiki ba kakkautawa, tare da bayar da bayanai ga sauran yankunan kan shirye-shiryensu na tunkarar matsalar.

Kungiyar ta yaba wa aikin da ake yi na kai hare-hare kan ‘yan fashin daji da masu satar mutane da kungiyar Boko Haram, musamman a arewa maso gabashi da wasu bangarori na arewa maso yammacin da arewa ta tsakiyar Najeriya.

Ta kuma karfafa wa dakarun tsaro da sauran hukumomin tsaro gwiwar ci gaba da yin hakan don a tabbatar da cewa an magance matsalar rashin tsaron baki daya cikin kankanin lokaci.

Kungiyar ta kuma karbi rahoto kan shirin samar da wutar lantarki na hasken rana ta kuma bayyana cewa an gabatar da batun samun filin da za a kaddamar da shirin kuma jihohin arewacin kasar na duba lamarin.
Taron ya kuma karbi bayanai kan ayyukan wasu kwamitoci da kungiyar gwamnonin arewa ta kaddamar tare da cewa an amince da shawarwarin da aka bayar inda za a gabatar da matakan da za a bi.
Kungiyar ta ce wasu gwamnonin arewacin Najeriya tun da fari sun bayyana ra’ayinsu na bin tsarin karba-karba zuwa ga shiyyoyi uku na kudancin kasar da nufin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a kasar.

Sai dai kuma kungiyar ta yi Allah-wadai da matsayar takwarorinsu na kudu cewa dole a mika shugabancin kasar ga yankin kudanci.

Kungiyar gwamnonin arewacin ta kuma duba batun karbar harajin VAT da ake ta yi a kasar.

“A matsayinmu na shugabannin da suka san ya kamata, duk da cewa mun san cewa batun na gaban, amma don sanar da mutane halin da ake ciki za mu bayyana wasu abubuwa kamar haka:
Hukuncin Babbar Kotun ya dasa ayoyin tambaya kan batun harajin VAT a kundin tsarin kasaGwamnatocin jihohin Lagos da Ribas sun sanya dokokinsu kan harajin VAT kuma sauran gwamnonin kudu sun nuna goyon baya kan hakanGwamnatocin wadannan jihohi sun rude suna sanya harajin kaya na VAT a matsayin harajin kasuwanciIdan kowace jiha ta sanya dokarta ta VAT, hakan zai jawo karbar haraji mai yawa daban-daban kuma hakan zai jawo durkushewar kasuwanci tsakanin jihohiWani rudanin shi ne kin duba hakan da kuma illar da hakan zai jawo. Abin da ya sa Legas ke kan gaba wajen samar da kasha 50 cikin 100 na Vat shi ne saboda kamfanonin sadarwa da bankuna da masana’antu da sauran harkokin kasuwanci duk a can cibiyoyinsu suke, wanda hakan ne ya sa ake alakanta ta da wacce take kan gaba wajen tara harajinKungiyar gwamnonin arewan ta ce za ta ci gaba da girmama wannan batu da yake gaban kotu a yanzu har sai Kotun Koli ta yanke hukunci karshe a kansa.

Sarakunan gargajiya sun yaba da kokarin da kungiyar gwamnonin arewa ke yi zuwa yanzu wajen warwware muhimman matsalolin da jihohin arewacin Najeriya ke fuskanta.
Kungiyar ta koka kan girman tuggun da wasu jami’an bangaren shari’a ke kitsawa ta wajen sakin miyagu daga gidan kaso da ba da belinsu

Tura Wa Abokai

An wallafa wannan Labari September 28, 2021 6:09 AM