Dalilin da ya sa ƴan Jigawa ke min lakabi da gwamnan a ‘buga lissafi, ayi shi dalla-dalla’ – Badaru

Gwamnan jihar Jigawa Mohammed Abubakar ya yi karin haske game da dalilin da ya sa mutanen jihar ke yi masa lakabi ‘Gwamnan ayi dalla-dalla, a buga lissafi’ tun da ya zama gwamnan jihar.

Abubakar ya yi wannan karin haske ne a lokacin da yake amsar bakuntar tsohon shugaban hukumar shige da fice ta ƙasa, Mohammed Babandede da ya kawo masa ziyara fadar gwamnatin jihar a makon jiya.

” Ni fa ba a yi min coge ko rufa-rufa, ko kuma zuƙe wajen lissafi, ina da abokai manyan ƴan kasuwa wanda sun san farashin komai. Idan abu naira 20,000 yake ba za a yi min zuƙe ba a kantara masa kudi a ce min naira 40,000 yake. Zan buga lissafi an gano.

” Wasu na yi min ganin na cika yin dole sai anyi komai dalla-dalla, ne kuma ba haka bane bana so ne a cuci gwamnati.

Babandede ya mika godiyarsa ga gwamna Abubakar sannan ya yaba masa kan jajircewa da yayi wajen bunƙasa jihar da kuma goyon bayan da ya bashi a lokacin da yake shugaban hukumar Imagirashon.

Wasu da dama sun musamman yan asalin jihar Jigawa sun bayyana cewa Babandede na daga cikin waɗanda ke kamun ƙafar ɗarewa kujerar gwamnan jihar idan Badaru ya kammala wa’adi n sa a 2023.

Sai dai kuma ya musanta haka cewa idan ma haka ne bayyana ra’ayi irin haka yayi wuri.