TAYA JONATHAN MURNAR CIKA SHEKARU 64: PDP ta kira shi gwarzon shugaban da ‘yan Najeriya ke tutiya da shi

Jam’iyyar PDP ta taya tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan murnar cika shekaru 64 a duniya, tare da bayyana shi a matsayin gwarzon shugaban da ‘yan Najeriya ke tuniya da tinƙaho da shi.

A ranar Asabar ce Jonathan wanda ya yi mulkin Najeriya tsawon shekaru shida a ƙarƙashin PDP ya cika shekaru 64 a duniya.

Jonathan ya yi mulki daga 2010 zuwa 2015, inda APC ta karɓi mulki daga hannun sa bayan an kayar da shi zaɓe.

PDP ta kira shi gwarzon shugaban da ‘yan Najeriya ke tutiya da shi.

Jam’iyyar PDP ta taya tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan murnar cika shekaru 64 a duniya, tare da bayyana shi a matsayin gwarzon shugaban da ‘yan Najeriya ke tuniya da tinƙaho da shi.

A ranar Asabar ce Jonathan wanda ya yi mulkin Najeriya tsawon shekaru shida a ƙarƙashin PDP ya cika shekaru 64 a duniya.

Jonathan ya yi mulki daga 2010 zuwa 2015, inda APC ta karɓi mulki daga hannun sa bayan an kayar da shi zaɓe.

A cikin wata sanarwar da Kakakin PDP Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Asabar a Abuja, jam’iyyar ta bayyana Jonathan a matsayin wani gwarzo mai kishin ƙasa, kuma jagora nagartacce.

Ta bayyana cewa irin sadaukar da kan da Jonathan ya yi wajen tabbatar da haɗin kan ƙasar nan ya kasance babban abin tarihi a Najeriya.

PDP ta ci gaba da cewa duk da Jonathan ya sauka daga kan mulki, har yau bai gajiya ba wajen ci gaba da aikin nuna kishi, gaskiya da ƙaunar ci gaban ƙasar nan fiye da duk wani muradi na sa da ya ke son cimmawa a rayuwa.

Ta ce tun ya na Mataimakin Gwamna, Gwamna, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Muƙaddashin Shugaban Ƙasa da kuma Shugaban Ƙasa, Jakadan Afrika duk ɗabi’un sa na dattako ya ke nunawa kuma su ke haska alƙiblar sa.

PDP ta bayyana irin ayyukan da Jonathan ya yi a fannoni daban-daban da kuma tarihin da ya kafa a lokacin zaɓen 2015, wanda hakan ya kai shi ga matakin ƙololuwa na zama gwarzon dattijo a Afrika ba ma a Najeriya kaɗai ba.