TAƁARƁAREWAR TSARO: ‘Yan bindiga sun haddasa haramta sayar da babura a faɗin jihar Neja

Gwamna Abubakar Bello na Jihar ya bada umarnin gaggauta hana sayar da babura a faɗin Jihar Neja baki ɗaya.

Sakataren Gwamnatin Jihar Neja Ahmed Matane ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Minna.

Sakataren Gwamnati Matane ya ce dokar hana sayar da baburan ta shafi babura samfuran Bajaj Bexer, Qiujeng, Honda ACE, Jingchen mai babban inji 185cc zuwa sama.

Ya ce gwamnati ta hana sayar dababuran ne domin ta daƙile ɓarnar masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da sauran ɓatagari a faɗin jihar.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin Neja ta yi tir da munanan ɓarnar da ‘yan bindiga ke yi ba ji ba gani a jihar Neja.

“Gwamnati na sane da irin mawuyacin halin da jama’a za su shiga sanadiyyar wannan doka, amma dai a yi haƙuri, saboda an ɗauki dokar ce domin yin hakan ne mafi alheri ga al’ummar jihar Neja.”

Yayin da gwamnati ta roƙi masu sayar da babura su kiyaye wannan doka, a gefe ɗaya ta umarci jami’an tsaro su tabbatar ana abin wannan dokar.

“Kuma gwamnatin Neja ta jaddada dokar hawa babur a Minna da kewaye daga ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma.”