TAUSAYI DA TAKAICI: Yadda mahara ke ƙona kayan abincin mazauna karkarar Zamfara

Manoma da dama a Jihar Zamfara na bada rahoton yadda mahara masu samame ke banka wa amfanin gonar su wuta, su kwashi na kwasa, su ƙona sauran a cikin gonaki.

Ba a nan su ka tsaya ba, waɗannan ‘yan bindiga na bin su har gida su ƙone masu rumbuna kuma su farfasa rumbunan.

Manoma da dama ko kuma mazauna yankin su da ‘yan uwan su, sun cika soshiyal midiya da hotunan yadda mahara suka ƙone masu kayan abinci ƙurmus.

Wannan mummunan al’amari kuma sai ƙar muni ya ke yi a kullum. Yayin da gwamnatin tarayya da jami’an tsaro ke shan alwashin ƙoƙarin magance lamarin.

Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna yankunan da aka fi yi wa wannan mummunar ɓarna sun haɗa da Gusau, Maru, Anka da Ƙaura Namoda.

Sama da shekaru 10 kenan yankin Zamfara na fama da ‘yan bindiga. Har abin ya kai ga mamaye yankin Arewa maso Yamma da ya haɗa da Jihar Katsina, Sokoto, Kaduna da Kebbi.

Garkuwa da mutane, kisan gilla da kisan ramuwar-gayya ya zama ruwan dare a yankunan. Yayin da Allah kaɗai ya san yawan biliyoyin kuɗaɗen da masu garkuwa suka karɓa daga hannun mutane, a matsayin kuɗin fansa.

Satar kayan abinci da satar shanu, fashi da makami da fyaɗe ga matan aure da ‘yan mata a zama ruwan dare a yankin.

Lamarin dai da farko ya fara ne a matsayin rikicin manoma da makiyaya, har ta kai ga yanzu ya zama ta’addanci muraran. Domin ta kai har jirgin yaƙin sojoji sai da ‘yan bindiga suka kakkaɓo.

Binciken Matsalar Tsaro wanda American Security Project Report ya gudanar, ya ce aƙalla mutum 200,000 sun gudu daga gidajen su cikin 2021, 77,000 sun tsallaka waje, musamman a Jamhuriyar Nijar domin neman wurin tsira da rayukan su.

Cikin makon jiya ne Gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari ya kafa kwamitin tantance ‘yan gudun hijira a Katsina, jihar da Shugaba Muhammadu Buhari ya fito domin a tallafa masu.

Dama kuma akwai dubban al’ummar Katsina da Sokoto waɗanda su ka tsere cikin Jamhuriyar Nijar.

Wani mai suna Mustapha Bala ɗan garin Bingi da ke Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Sokoto, amma ya ke zaune cikin Gusau, ya shaida wa wakilin mu cewa mahara sun banka wa kayan gonar kawun sa da na maƙwautan kawun nasa wuta.

“Da farko har murna muka riƙa yi lokacin da mu ke girbi. Gonar makekiya ce wadda mu ka shuka wajen soya. Amma a ranar da kawu na da maƙwautan sa ke duba yawan wajen da aka girbe, sai ‘yan bindiga suka kewaye gonar, suka kore su. Su ka banka wa waken wuta baki ɗaya.”

Kamar yadda su ka yi a Bingi, haka su ka yi wa manoma a Kanoma, har ta kai wani manomi ya shaida wa wakilin mu cewa shi ba zai yi noma a shekara mai zuwa ba.

A garin Magami cikin Karamar Hukumar Gusau, Almustapha Abdullahi ya sanar da wakilin mu cewa mahara sun ƙona masa masara kuma sun yi garkuwa da masu aiki a gonar.

Sai dai kuma duk wannan ɓarna da ake yi wa mazauna karkara, Kakakin ‘Yan Sandan Zamfara, Mohammed Shehu ya ce ba su da labari. Ba a kai masu rahoto ba.