Majalisar dokokin Jigawa ta karyata labarin yunkurin tsige Kakakinta

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin Jihar Jigawa Muhammad Adamu, ya karyata jitajitar cewar mambobin majalisar suna yunkurin tsige Kakakinta Idris Garba.

Malam Adamu ya shaidawa manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa cewa labarin da aka buga a wasu kafofin yada labarai cewa za’a tsige sifika labarin konzon kurege ne kirkiranran labari ne.

Yace wasu ne kawai suke yunkurin batawa Jihar da kuma majalisar suna. Muna zaman lafiya da fahimtar juna da Kakakin majalissar da kuma gwamnatin Jihar ta Jigawa.

Malam Adamu yace majalisar ba ta yawan zama saboda aiyukan cigaban al’umma yasa take yawan zuwa taro irin na samina a wajen Jihar Jigawa.

” Ina zargin gwamna Muhammad Badaru da Kakakin majalisar suna takun tsaka ne akan yunkurin shi Kakakin na neman kujerar gwamna a shekarar zabe na 2023″.