TSADAR FETUR: Gwamnati ta ce gidajen mai sun fara ƙara kuɗi saboda sai sun sayi dala daga hannun ‘yan canji su ke biyan hukumomi kuɗin dako

Gwamnatin Tarayya ta ce gidajen mai yanzu a wasu jihohi sun ƙara kuɗin mai, saboda masu safarar fetur na biyan Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa da dala ne, ba da naira ba.

“To babbar matsalar ita ce yadda ba su iya samun dalar a farashin gwamnati, tilas sai sun saya da tsada a kasuwannin ‘yan canji.”

Wannan ya sa a wasu garuruwan ana samun ƙarin kuɗin litar man fetur fiye da farashin da gwamnati ta ƙayyade.

Shugaban Hukumar NMDPRA, Faruq Ahmed ne ya bayyana wa manema labarai haka a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan ya fito daga taron ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata.

A yayin ganawar ce kuma ya ce a lokacin da ya zama shugaban hukumar a cikin Oktoba, ya gano dillalan man fetur da manyan masu gidajen mai na bin gwamnatin tarayya bashin naira sama da biliyan 100.

Ya ce bashin ya kama tun daga 2017 har zuwa Oktoba, 2021.

Premium Times Hausa ta buga labarin cewa Gwamnatin Buhari za ta tsula farashin litar fetur a cikin 2022 har zuwa naira 340. Amma za a rika bai wa talakawa naira 5000 su rage raɗadin ƙuncin rayuwa.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta cire kuɗin tallafin man fetur, wanda hakan na nufin za a ƙara kuɗin litar fetur.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, a lokacin ƙaddamar da wani shiri na Bankin Duniya a Najeriya.

Sai dai kuma ta ce gwamnatin tarayya za ta zaƙulo mutane miliyan 30 zuwa 40 da su ka fi kowa talauci a kasar nan ta riƙa ba su naira 5,000 kowace Wata, domin rage masu raɗaɗin ƙuncin rayuwar da za su iya afkawa a ciki nan gaba idan an ƙara wa fetur farashi.

Ta ce rarar kuɗaɗen da za a riƙa samu ce za a duba sannan a san ko adadin mutum nawa ne za su riƙa amfana da tallafin.

Idan ba a manta ba, Bankin Bada Lamuni na Duniya, IMF ya shawarci Najeriya ta gaggauta cire tallafin mai domin ta ƙara samun kuɗin shiga. Kuma ta rage kashe kuɗaɗe a ayyukan da ba masu muhimmanci ba.

Bankin IMF ya shawarci Najeriya ta gaggauta cire tallafin da na kuɗin wutar lantarki a farkon 2022.

Idan Gwamnatin Najeriya ta yi amfani da shawarar Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) har ya cire tallafin man fetur da na wutar lantarki a farkon 2022, ‘yan ƙasar nan za su shiga sabuwar shekara cikin halin ƙuncin rayuwar da ta fi ta shekarar 2021 da ake ciki.

Kai tsaye ba wani abu ba ne cire tallafin man fetur da na wutar lantarki, ma’ana ita ce a ƙara wa farashin litar man fetur da wutar lantarki kuɗi.

IMF ta gargaɗi Najeriya cewa yawan kuɗaɗen da ta ke kashewa idan auna su da waɗanda ta ke samu, to za’a ci gaba da samu wawakeken giɓi a kowace shekara, kamar irin wanda aka samu a bana cikin 2021, to haka ma za ta kasance a shekara mai zuwa.

“Amma idan aka cire tallafin fetur da na kuɗin lantarki, an kamo hanyar saisaita matsalolin ƙaranci kuɗi a hannun gwamnati kenan.

“Amma kuma tilas sai ita gwamnatin ta bijiro wasu tsare-tsaren da za ta rage wa talakawa tsadar rayuwa, sakamakon matsin da za su shiga idan an ƙara kuɗin fetur da kuɗin wutar lantarki. Kuma dama akwai wannan sharaɗin a cikin Sabuwar Dokar Man Fetur ta 2021 cikin watannin baya.”

IMF ya ƙara da cewa, tafiyar-hawainiyar da sabon tsarin canjin kuɗaɗe ke yi, tare da rashin tabbas na kasa maido maƙudan kuɗaɗen da ɓarayin gwamnati su ka sace suka ɓoye a waje, ya rage ƙarfin yawan shigowar jari mai nauyi a Najeriya.”

Wasu ƙarin matsalolin da tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da fuskanta, a cewar IMF, sun haɗa da ƙarancin kayan da Najeriya ke fitarwa waje.

A kan haka sai IMF ta nemi Najeriya ta fito da wani tsari da zai daɗe tsawon lokaci ya na hana kuɗaɗen ajiyar Najeriya a waje raguwa.