SUN YI TUTSU: Majalisar Dattawa ta ƙi ƙara yi wa Dokar Zaɓe Kwaskwarima, kamar yadda Buhari ya nemi su yi

Majalisar Dattawa ta yi fatali da wani ƙudirin neman su ƙara yi wa Sabuwar Dokar Zaɓe Kwaskwarima, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi ta yi.

A ranar Laraba ce dai mambobin Majalisar Dattawa ɗaukacin su suka yi amincewa da wani ƙudiri da aka karanta, domin a yi masa karatu na biyu.

Ƙudirin dai na tafiya ne kafaɗa-da-kafaɗa da buƙatar Shugaba Buhari ta a sake yi wa Dokar Zaɓe kwaskwarima, domin a cewar Buhari, ya gano wasu giɓin da babu haƙora a cikin bakin dokar.

A cikin watan Fabrairu ne dai Buhari ya nemi Majalisar Dattawa cewa ta cire wasu ƙudiri na ‘Clause 84(12)’, na cikin Dokar.

Kudirin dai shi ne wanda ya haramta wa duk wani mai riƙe da muƙamin gwamnati na siyasa ya yi zaɓe ko a zaɓe shi domin tsayawa wata ta takara a wurin gangamin taron siyasa.

Buhari ya ce dokar ko ƙudirin ya tsuyen ‘yancin waɗanda aka hana ɗin.

Jam’iyyar PDP ta ƙi yarda a cire ƙudirin, inda ta gaggauta sheƙawa kotu.

Buhari ya nemi su cire shi ne bayan ya sa wa Dokar Zaɓen hannu, amma PDP da ƙungiyoyi da dama ba su amince ba.

PDP ta nemi a kotu ta hana Buhari sake gyarawa ko yin kwaskwarima ga sabuwar dokar zaɓe.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya yanke hukuncin cewa tunda daftarin ƙudirin ya rigaya ya zama Doka, to babu wani mahalukin da ya isa ya ƙara yi masa kwaskwarima, ba tare da bin ƙa’idar da doka ta shimfiɗa ba.

Ekwo ya yanke hukuncin hana Buhari, Ministan Shari’a ko Majalisar Dattawa yi wa sabuwar dokar katsalandan.

Majalisar Dattawa Ta Yi Wa Buƙatun Buhari Tutsu:

Sanata Adamu Aliero ne ya nusashshe da Majalisar Dattawa cewa akwai batun jingine ƙudirin har sai lokacin da kotu ya jingine umarnin ta.

Sanata Lawan ya ce duk da kotu ta yi gargaɗi, hakan ba zai hana Majalisar Dattawa yi masa kwaskwarima ba.

Daga nan masu adawa da ƙoƙarin yin kwaskwarimar, irin su Shugaban Marasa Rinjaye, Enyinnaya Abaribe ya tashi ya fara ragargazar Shugaban Majalisar Dattawa, ya na mai ce masa maƙiyin dimokraɗiyya.

Daga nan Abaribe ya roƙi sauran mambobin Majalisar Dattawa kada su bari a yi wa ƙudirin karatu na biyu.

A ƙarshe dai waɗanda su ka nemi a yi fatali da shi, kamar yadda Babbar Kotun Tarayya ta yi gargaɗi, su ne su ka yi rinjaye.

Dajin Da Aka Keto Kafin Buhari Ya Sanya Wa Sabuwar Dokar Zaɓe Hannu:

Shugaban Ƙasa ya sake gano wani giɓi a zubin haƙoran Sabuwar Dokar Zaɓe.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa har yanzu dai akwai sauran baddalallun hukunce-hukunce da tanade-tanade a cikin Sabuwar Dokar Zaɓe, wadda ya sa wa hannu a ranar Juma’a.

Buhari ya yi bayanin yayin da ya sa wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe hannu, inda yanzu ya zama Sabuwar Dokar Zaɓe.

Ya yi bayanin da sa hannun a gaban Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila da wasu manyan jami’an gwamnati.

Shugaban ya gode wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya, ganin yadda su ka sake yi wa ƙudirin kwaskwarima daidai yadda ya ke so.

Ya ce dokar za ta ƙara inganta martabar zaɓe a Najeriya, musamman ta sabuwar hanyar yin amfani da kayan sadarwa da na’urori na zamani domin tabbatar yin komai ƙeƙe-da-ƙeƙe a lokacin zaɓe.

Ƙorafe-ƙorafen Buhari:

Sai dai kuma Buhari ya yi ƙorafi a kan Sashe na 84(12).

Ga Abin Da Sashen Ya Gindaya:

“An hana duk wani mai riƙe da muƙamin gwamnati wato muƙaman siyasa a Tarayya, Jiha ko Ƙaramar Hukuma ya yi zaɓe ko a zaɓe shi a wurin Taron Gangamin Jam’iyya ko Zaɓukan Shugabannin Jam’iyya na jiha ko ƙaramar hukuma ko tarayya.”

Buhari ya ce wannan sabuwar dokar ta ci karo da wata dokar da ke cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Ya ce dokar ta tauye wa masu riƙe da muƙaman ‘yancin su na yin zaɓe ko a zaɓe su a shugabancin jam’iyyu.

Daga nan sai Buhari ya yi nuni da Sashe na 40 da na 42 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

“Doka ta amince wanda ke riƙe da muƙamin gwamnati zai iya ajiye aikin sa kwanaki 30 kafin ya tsaya takarar wani muƙamin shugabanincin jam’iyya, wato kafin zaɓen.” Inji Buhari.

Sai dai kuma ya ce duk da wannan cikas ɗin, ya sa wa dokar hannu, saboda la’akari da muhimmanci, ƙurarren lokaci da sauran su.

Yadda Majalisar Dattawa Ta Ƙara Yi Wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe Wata Kwaskwarima:

A wani ƙwarya-ƙwarya kuma taƙaitaccen cimma matsaya da Majalisar Dattawa ta yi a ranar Talata, ta sake yi wa Ƙudiri na 84 na Dokar Gyaran Zaɓe Kwaskwarima.

An yi kwaskwarima ɗin ce ta yadda idan Shugaba Muhammadu Buhari ya sa mata hannu, za ta bai wa jam’iyyun siyasa damar kowace ta bi tsarin da ya fi daidai a gare ta wajen zaɓen fidda gwani.

A cikin ƙudirin gyaran dokar zaɓen dai wanda Majalisar Dattawa ta sa wa hannu cikin 2021, sun rattaba cewa zaɓen fidda gwanin kowace jam’iyya zai kasance na ‘yar-tinƙe ce.

Sai dai kuma Shugaba Muhammadu Buhari bai amince da wannan ƙudirin ba.

Dalili kenan ya maida wa majalisa domin ta yi masa kwaskwarima.

Yayin da Majalisar Dattawa ta amince da zaɓen kai-tsaye ko ‘yar tinƙe ko kuma tsayar da ɗan takara a bisa tsarin yarjejeniyar amincewa, ita kuwa Majalisar Tarayya ba ta amince da fitar da dan takara ta hanyar cimma yarjejeniyar tsayar da mutum ɗaya ba tare da zaɓe ba (wato consensus candidate).

Farkon makon jiya ne Majalisar Dattawa ta yi wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe Kwaskwarima kamar yadda Shugaban Muhammadu Buhari ya nemi ta yi, kafin ya sa mata hannu

Gyare-gyaren Da Majalisar Dattawa Ta Yi Wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe:

Majalisar ta fara yin gyaran gaggawa kan Ƙudiri na 87, wanda ya yi magana kan irin zaɓen fidda-gwanin ‘yan takara daga kowace jam’iyyar siyasa.

A yanzu an amince kowace jam’iyya ta zaɓi gwanayen ta bisa tsarin ‘yar tinƙe, ƙato-bayan-ƙato ko zaɓen game-gari.

Da farko dai Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe ya amince a yi zaɓen kai-tsaye, ba na wakilan jam’iyya ba, wato ‘delegates’.

Wannan tsari ne ake kai a ƙasar nan, wanda kuma ƙoƙarin kawar da shi a zaɓen 2023 bai yi nasara ba, biyo bayan fatali da tsarin zaɓen kai-tsaye da Buhari ya yi bisa dalilin cewa zai ci maƙudan kuɗaɗe wajen gudanarwa.

An amince da Ƙudiri na 84, wanda ya bada damar ko jam’iyya ta yi zaɓen kai-tsaye ko kuma tsarin wakilan jam’iyya, wato ‘delegets’.