TARON MAJALISAR ƊIKIN DUNIYA: Abin da Bawan EFCC ya shaida wa ƙasashe 192 kan manyan barayin Najeriya

Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa, ya nemi haɗin kan ƙasashen duniya 192 wajen ganin Najeriya ta dawo da maƙudan kuɗaɗe da tulin kadarorin da barayin gwamnatin Najeriya su ka sace, su ka kimshe a ƙasashe daban-daban.

Bawa ya yi wannan bayani ne a lokacin daya ke jawabi a Taron Majalisar Dinkin Duniya a Taron Musamman na 32 na Majalisar Dinkin Duniya, a birnin New York, na Amurka, a ranar Alhamis.

Najeriya mamba ce a Majalisar Dinkin Duniya, tare da sauran mambobi 192.

An shirya taron musamman “Taron Daƙile Haryoyin Cin Hanci da Rashawa Tsakanin Ƙasashe”, a ranakun 2 zuwa 4 Ga Yuni.

“Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da garken barayi su ka saci arkizin ta su ka kimshe wasu ƙasashe daban-daban.

“Saboda haka Najeriya na buƙatar hadin kan waɗannan ƙasashe su taimaka wajen ganin an dawo wa Najeriya da waɗannan kuɗaɗe da kadarori daga ƙasashen da aka boye su.

“Sannan kuma Najeriya na buƙatar haɗin kan waɗannan ƙasashe wajen ganin sun taimaka an daƙile hanyoyin da ake satar kuɗaɗe daga ƙasashe masu tasowa ana kai su ƙasashen da su ka ci gaba.”

“Haka kuma Najeriya ta buƙaci ƙasashen duniya su yi amfani da shirin yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙadashen su.

Ana hasashen cewa Najeriya na a sahun gaba inda manyan barayin gwamnati su ka ci satar kuɗaɗen gwamnati su na boyewa ƙasashen ƙetare.

An haƙƙaƙe cewa tsohon Shugaban Ƙasa na Mulkin Soja, Janar Sani Abacha da iyalan sa sun sace dala biliyan 5 a zamanin mulkin sa.

Fiye da shekaru 20 bayan mutuwar Abacha, har yau Najeriya na ta haƙilon ganin ta maido kuɗaɗen da Abacha da iyalan sa su ka sace.

Amma kuma an karbo kuɗaɗen da aka boye a Amurka, Switzerlnad Rhodes Island da New Jersey.

Wani rahoto da Brookings, wata ƙungiyar binciken kuɗaɗen sata ts buga cikin 2020, ta ce tsaanin 1980 zuwa 2018, an sace dala tiriliyan1 daga wasu ƙasashen Afrika an boye a manyan ƙasashe.

“Ƙasashen sun haɗa DR Congo, Habasha da Najeriya.”