Kamfanonin sadarwar sun bi umarnin gwamnati, sun toshe damar shiga Twitter

Ƙungiyar kamfanoni masu lasisin layukan sadarwa a Najeriya, ALTON, ta ce ta samu umarni daga Hukumar Sadarwa ta NCC, mai kula da masana’antu, kan dakatar da shiga shafi Twitter.

Shugaban ALTON, Gbenga Adebayo ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai a Legas, ranar Asabar.

Matakin ba zai rasa nasaba da dakatar da ayyukan Twitter da aka yi ranar Juma’a ba, kwana biyu bayan da babban kamfanin na sada zumunta ya goge wani sakon da aka wallafa a shafin Shugaba Buhari.

A cewar jawabin ƙungiyar,
“ALTON ta gudanar da cikakken bincike kan bukatar bisa ka’idojin da duniya ta yarda da su.

“Dangane da tanade-tanaden da suka shafi maslahar ƙasa a cikin Dokar Sadarwar Najeriya, 2003, kuma a tsakanin ka’idojin lasisi da masana’antar ke aiki a ƙarkashinta; membobinmu sun yi aiki daidai da umarnin NCC.

“Za mu ci gaba da yin hulda da dukkan hukumomin da abin ya shafa da masu ruwa da tsaki kuma za mu yi aiki kamar yadda NCC za ta ci gaba da jagoranci,” in ji Mista Adebayo

Ya ce kungiyar za ta ci gaba da jajircewa wajen tallafawa gwamnatin Tarayyar Najeriya da kuma kare hakkin ‘yan kasa.