TALLAFIN NAIRA 5,000 Ga TALAKAWA MILIYAN 40: ‘Shafa Labari Shuni’ Ko ‘Hikayoyin Shehu Jaha’?

An shafe shekaru gwamnatin Najeriya ta kan zirin siraɗin ƙoƙarin cire tallafin man fetur. A duk lokacin da aka yi ƙoƙarin cirewa, ‘yan Najeriya kan fusata. Sai dai a wannan karon, Gwamnatin Buhari za ta cire ɗin, domin har ma ta saka batun cire tallafin a cikin kasafin 2022.

Gwamnatin Tarayya na ganin cewa tallafin fetur na taimakawa ga talakawa, domin idan fetur ya yi tsada, su ne ke fin shan wahalar ƙuncin rayuwa.

Sai dai duk da wannan, cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe na duniya, irin su IMF, su a ganin su, tallafin fetur na hana ƙasar nan ci gaba tare da kasa samar wa ‘yan ƙasa ayyukan inganta rayuwa da ci gaba.

Tsakanin 2006 zuwa 2018, Najeriya ta kashe naira tiriliyan 10 wajen biyan kuɗin tallafin mai. Wani bincike da gwamnatin Birtaniya ta gudanar, ya nuna cewa kuɗin da Najeriya ta kashe kan tallafin mai a wadancan shekarun, sun zarce kasafin kuɗin Najeriya na fannin ilmi da na fannin tsaro baki ɗaya daga 2006 zuwa 2018.

Hukumar NNPC ta ce a cikin watanni takwas su ka gabata, ta kashe naira biliyan 816 wajen cike gurbin tallafin fetur.

An Ki Cin Biri An Ci Kare: Za A Daina Biyan Tallafi Ko Koma Biyan Wani Sabon Tallafi:

Sabuwar Dokar Fetur ta 2021 ta haramta biyan tallafin fetur daga tsakiyar 2022, kamar yadda IMF ya bada shawara.

Amma kuma Gwamnatin Tarayya ta ce za ta riƙa biyan talakawa miliyan 40 naira 5,000 kowane wata, matsayin kuɗin rage masu raɗadin tsadar kuɗin shiga motar haya da babu makawa sai ya nunka, idan aka ƙara wa fetur kuɗi.

Albishir Ɗin Tallafin Naira 5,000 Ko Hikayoyin Shehu Jaha?:

Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed wadda ta fara yin albishir ɗin za a riƙa biyan naira 5,000 idan an ƙara kuɗin fetur, ta ce amma fa sai idan akwai kuɗi a ƙasa sannan za a biya.

Sannan kuma Zainab ta ta yi tiyata, amma ta manta almakashi a cikin majiyyaci, domin ta manta cewa a cikin kasafin 2022 babu batun za a riƙa bai wa talakawa miliyan 40 naira 5,000 kowanen su a duk wata.

Sannan kuma cewa ta yi watanni shida kacal za a yi ana biyan, idan ma akwai kuɗin da za a biya su ɗin.

Wannan labari daga bakin Minista Zainab, zai iya zama shafa labari shuni, don kawai a yaudari talakawan Najeriya.

Domin idan za a biya talakawa miliyan 40 naira 5,000 har tsawon shekara ɗaya, to za a kashe masu naira tiriliyan 2.4 kenan.

Naira tiriliyan 2.4 kuwa daidai ta ke da kashi 15% bisa 100% na kasafin kuɗin Najeriya na 2020.

Idan aka dubi adadin naira biliyan 150 na tallafin fetur da gwamnatin tarayya ke biya a duk wata, wato naira biliyan 150, a shekara gwamnati na biyan naira tiriliyan 1.8 kenan, kuɗin da kusan rabin abin da gwamnatin za ta riƙa kashewa ne wajen biyan talakawa naira 5,000.

Wannan na nuna cewa idan ma gwamnatin Buhari ta cire kuɗin tallafin mai, aka tsula wa fetur kuɗi, to ko ranyo ba za ta iya tarawa ba domin yin ayyukan da ake son yi ɗin saboda cire tallafin fetur.

Sannan kuma yayin da Minista Zainab ke cewa samun haraji mai yawa ne matsalar Najeriya, a gefe ɗaya kuma Najeriya ba ta komai sai ciwo bashi, sannan kuma ta ƙi rage hanyoyin da gwamnati ke kashe maƙudan kuɗaɗe da ba su wajaba a riƙa kashewa ba.

Majalisar Dattawa da ta Tarayya, ɓangaren ayyukan yau da kullum a ofisoshin gwamnatin tarayya na daga wuraren da gwamnatin tarayya ke ɓarusa da kuɗaɗe ta inda bai kamata ba.