Ranakun aiki a ofis sun koma Litinin-Alhamis a Kaduna, za a rika aiki daga gida ne ranar Juma’a – El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Nasirl El’Rufa’I ya bayyana cewa ma’aikatan gwamnati a jihar za su rika zuwa aiki sau hudu a mako cewa kowa zai yi aiki daga gida ranar Juma’a.

El-Rufa’I ya sanar da haka ne a wani sako wanda mai bashi shawara kan harkokin yada labarai Muyiwa Adekeye ya fitar ranar Litinin a garin Kaduna.

Bisa ga sabon tsarin, ma’aikata za su rika zuwa aiki ne daga ranakun Litinin zuwa Alhamis daga karfe 8 na safe zuwa karfe 5 na yamma.

Ya ce wannan tsari wanda zai shafi fannin dake zaman kansu da gwamnati ta shigo da shi zai fara aiki ranar 1 ga watan Disemba 2021.

“Malaman makaranta, jami’an lafiya da manyan ma’aikatan gwamnati ne kawai za su ci gaba da zuwa aiki yadda suka saba yi.

Gwamnati ta kirkiro wannan tsari ne domin bai wa ma’aikata daman hutu domin inganta aikinsu da samun lokaci domin zuwa gona da kasancewa tare da iyalan su a gida.

Gwamnati ta amince da wannan tsari bisa ga darasin da ta koya daga lokacin da cutar korona ta bullo inda dole wasu ma’aikata ke aiki daga gida.

El-Rufa’I ya kara da cewa gwamnati za ta samar wa ma’aikata da Intanet domin su ci gaba da aiki a lokacin da suke gida batare da an samu wata matsalaba.

Ya ce tsarin zai fara aiki yadda ya kamata a watan Janairu 2022 sannan hakan zai bai wa fannin dake zaman kansu damar gudanar da aiyukansu suma bisa wannan tsari.