ZAMFARA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Yadda mahara suka kashe mutum hudu a harin hanyar Tsafe-Gusau

A ranar Lahadi da yamma ne ‘yan bindiga suka datse hanyar Tsafe – Gusau suka kashe mutum hudu a kaukan Karazau da Gidan Kaura dake karamar hukumar Gusau jihar Zamfara.

Karaza da Gidan Kaura kauyuka ne dake iyaka da garin Gusau.

Majiya da dama sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigan sun tare hanyar Tsafe, Funtua da Zaria zuwa Kaduna da Abuja domin hana mutane neman dauki ko sanar wa jami’an tsaro harin da za su yi a wuraren.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Kwarin Mai Saje dake karamar hukumar Tsafe saboda mazauna kauyen sun kasa biyan Naira miliyan uku kudin harajin da ‘yan bindigan suka saka musu.

‘Yan bindigan sun yi wa mata fyade, sun saci kayan mutane masu daraja sannan sun yi garkuwa da akalla mutum shida a wannan kauyen.

Haka na daya daga cikin hare-haren da ‘yan bindiga suka saba yi a jihar Zamfara sannan ‘yan bindigan na haka ne duk da matakan dakile aiyukkan mahara da gwamnati ta dauka a jihar.

Kai wa mutane hari babu kakkautawa da ‘yan bindiga ke yi ya sa Babbar Kotun Tarayya ta ayyana ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane cewa su ma ‘yan ta’adda ne, kamar Boko Haram da ISWAP.