Sojoji sun hallaka ƴan bindiga a wasu luguden wuta a Kaduna

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sojoji sun hallaka fiye da ‘yan bindiga 50 a wani harin sama da ƙasa da suka kai a yankin Saulawa da Farin Ruwa da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ta ce nasarar ta biyo bayan hare-haren da jami’an tsaron haɗin gwiwa da jiragen sojin saman Najeriya suka kai a dazukan Dogon Dawa da Damari da Saulawa.

  • Facebook

    Twitter

Labarin bayaƳan sanda sun cafke wani da ake zargi da kisan kai saboda wata karuwa

Hausa Daily Times ingantacciyar kafar yaɗa labarai ce da ke da ƙwararrun ma’akata ƙarƙashin jagorancin ƙwararrun ƴan jarida.