Sama da naira miliyan 20 aka biya ƙudin fansa kafin Ƴan Bindiga suka sake ni – Sarkin Ɓungudu

Ƴan fashin daji da suka kama Sarkin Bungudu, dake Jihar Zamfara, Hassan Attahiru, sun karbi kudi fiye da miliyan N20 kafin sakin Sarkin bayan ya shafe kwanaki 32 a daji.

Yan Bindigar sun tare tawagar Sarki ne a Jihar Kaduna cikin watan jiya akan hayarsa ta zuwa Abuja. An sace shi sati biyu kafin a yanke kafofin sadarwa ta waya a wasu bangare na Jihar Kaduna.

Yanke kafafen sadarwar a Kaduna da wasu Jahohin Arewa na daya daga cikin matakan da gwamnonin yankin suka dauka domin magance ayukan Yan Bindigar da suka addabi yankin.

Yanke kafar sadarwar a Kaduna ya kawo cikas wajen jinkirin magana da Yan Bindigar ta waya domin kawo kudin fansa.

Wane Basarake daga masarautar ta Bunguda wanda baisu a bayyana sunansa ba yace sai da fara biyan Naira miliyan N20 kafin kafin a yanke kafar sadarwar.

Bayan yanke kafar sadarwar, Yan Bindigar sun ringa yawu wajen neman sabis a inda suka bukaci a kara musu miliyan N100 bayan miliyan N20 da aka basu tun farko.

Mutumin da ya kai kudin fansa na Naira miliyan N20 na farko ya tafi cikin dajin ne akan babur daga garin Rigachikum inda yayi tafiya har na kusan awa uku, amma duk da haka daya ji bai sami ganinsu sai ya dawo da kudin garin Kaduna.

Amma yana shigowa gari sai Yan Bindigar suka kuma kiransa suka ce masa ya dawo cikin daji ya kawo kudin, haka ya kuma kumawa ya basu kudin a cikin buhu na bagko.

Duk da haka Yan Bindigar sunki su sake Sarkin sai da aka kara musu wasu miliyoyin nairori kafin suka sake Shi, inji shi majiyan namu.

.