Ƴan Sanda na binciken jami’in da aka gani yana jefa kuri’a a zaɓen shugabannin jam’iyya a Kano

Babban jami’in Yan Sanda maikula da shiya ta ɗaya (Zone one ) dake Kano, Abubakar Bello, ya bada umarnin a yi bincike akan Jami’i da aka gani yana jefa kuri’a a zaɓen shugabannin jam’iyya na Kano da gudanar ranar Asabar.

Anyi zaben ne a babban Filin wasa na Sani Abacha dake a Kofar Mata a Kano.

Kakakin Ƴan Sanda mai kula da sashe na daya (zone one) Abubakar Zayyanu, ya bayyana sunan Ɗan Sandan da Bashir Muhammad, yace an turashi aikin bada tsaro ne a gidan gwamnatin Jihar Kano.

Amma anga Bashir dumu-dumu a cikin hoto yana jefa kuri’a, a gefensa tareda Abdullahi Abbas, wanda aka zaba a ranar Asabar a matsayin shugaban APC a Kano.

Kakakin na Ƴan Sanda yace an baiwa sashe na musanman (Zonal X-Squad) da su binciki wannan ɗan Sanda.

Sanarwar tace an tura Ɗan Sandan ne aiki a gidan gwamnati a inda daga bisani aka tura shi ofishin Abdullahi Abbas domin bashi kariya.

Idan har ta tabbata yayi laifi za’a masa hukuncin da ya dace dashi kuma za’a bayyanawa mutane dukkanin mataki da aka dauka, inji Kakakin Yan Sanda mai kula da sashe na daya.