SHUGABAN ƘASA: Za mu ba Jonathan damar fitowa takarar zaɓen 2023 idan ya dawo APC -Sakataren APC na Ƙasa

Sakataren Riƙo na Ƙasa na Jam’iyyar APC, John Akpanudoedehe, ya bayyana cewa za sha dibirin labarai kenan idan tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan ya sauya sheƙa, ya koma jam’iyyar PDP a zaɓen 2023.

Da ya ke bayani a gidan Talabijin na Channels, Akpanudoedehe ya ce ba shi da wani cikakken labarin shirin Jonathan zai koma PDP.

“Amma dai idan ya dawo cikin mu a APC, to za a ba shi muƙami na musamman, daidai da manyan iyayen jam’iyya da su ka kafa ta. Za a ba shi damar fitowa takarar shugabanci a zaɓen 2023 kamar yadda za a bai wa kowa dama.”

An daɗe ana raɗe-raɗin cewa Jonathan zai koma APC, duk kuwa da shi kan sa ya ce ya daina shiga lamarin siyasa, zai zauna ne ya maida hankali wajen ayyukan jinƙai waɗanda ya ke yi a cikin al’umma, musamman a Afrika.

A ranar Laraba ɗin nan ce kuma Kakakin Yaɗa Labarai na Jonathan, Ikechukwu Eze ya bayyana cewa labarin da ake yaɗawa wai Jonathan zai koma APC, na bogi ne, ba gaskiya ba ce.

Duk da cewa Shugaba Buhari zai kammala wa’adin mulkin sa a 2023, har yau APC mai mulki ba ta tsaida ko nuna ɗan takarar ta shugaban ƙasa ba.

Sai dai ‘yar manuniya na nuni da cewa mulki ko kuma a kudu za a bayar da takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC ɗin. A kudun ma an fi hanƙoron a bai wa yankin Kudu maso Yamma.

Jonathan dai zango ɗaya ya yi, inda Buhari ya kayar da shi a ƙoƙarin na ƙarasa zangon sa na biyu.

Bayan an kayar da shi, Jonathan ya sha yabo a Najeriya, Afrika da duniya baki ɗaya, saboda bai nuna fifikon son zama kan kujerar sa ko a mutu ko a yi rai ba.

Daga baya Gwamnatin Buhari ta jawo shi a jiki, aka riƙa tura shi ƙasashen da ake husumar shugabanci domin sasantawa. Kuma ya na wakiltar Najeriya a zaɓuka a ƙasashen da ake so dimokraɗiyya ta ɗore a Afrika.

Har yau ita ma PDP ba ta nuna ɗan takarar ta a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba.

Jonathan A APC: Biri Ya Yi Kama Da Mutum:

Ko dai Goodluck Jonathan bai nuna sha’awa ko neman komawa APC ba, jama’a da dama na ganin cewa APC na zawarcin sa ta ƙarƙashin ƙasa.

Watannin baya da hayaniyar komawar sa APC ta fara fitar da hayaƙi, jiga-jigan PDP sun yi tattaki har gidan sa a Abuja, inda ya jaddada masu cewa labarin ba gaskiya ba ne.

Ana Wata Ga Wata: A ranar Laraba kuma Majalisar Zartaswa ta amince a kashe Naira biliyan 38.4, domin kammala wasu ayyukan kwangilolin titina a jihohi biyar da aka bayar tun lokacin Jonathan, ciki kuwa har da Bayelsa jihar sa ta haihuwa.

A taron wanda Shugaba Buhari ya jagoranta, an amince Gwamnatin Buhari za ta kashe Naira biliyan 38.4 domin kammala aikin titinan Gwamnatin Jonathan a Anambra, Benuwai, Bayelsa, Imo da Nasarawa.

Gwamnatin Tarayya ta amince a kashe Naira biliyan 38.4, domin kammala wasu ayyukan titinan da aka bayar a lokacin gwamnatin Jonathan, amma ba a biya wasu kuɗaɗen ba, wasu ayyukan kuma ba a fara ba saboda rashin kuɗi a lokacin.

Minsitan Ayyuka da Gida Babatunde Fashola ne ya bayyana wa manema labarai haka, a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan kammala taron Majalisar Zartaswa a ranar Laraba.

Fashola ya ce ayyukan titinan ba sabbi ba ne, duk waɗanda aka bayar da kwangilar su ne a lokacin gwamnatin Jonathan, amma ba a biya kuɗaɗen ba. Wasu kuma ko farawa ba a yi ba, saboda rashin kuɗi.

“Za a kammala ayyukan amma yawancin su duk sai da aka sake duba yarjejeniyar kwangilar, aka yi ƙarin kuɗaɗe, saboda tsadar kayan aiki tsakanin 2014 zuwa yanzu.”

Daga cikin titinan da Fashola ya bayyana, akwai aikin kilomita 13 a kan titin Anacha zuwa Owerri har ya dangana da Nnewi a jihar Anambra.

“An bayar da kwangilar tun cikin 2011, amma ba a biya kuɗin kwangilar ba. Yanzu an amince a biya domin a ƙarasa aikin, bayan an sake bibiyar kuɗaɗen aikin zuwa Naira miliyan 488,980,891.

“Sai kuma aikin titi mai tsawon kilomita 20 wanda ya haɗa da maida titin zuwa Yenagoa mai falan-biyu har zuwa Otuake.

“Tun cikin Disamba, 2014 Gwamnatin Jonathan ta bayar da aikin, amma ya samu tsaiko saboda hare-haren ‘yan takifen Neja-Delta da kuma ƙarancin kasafin kuɗi.” Inji Fashola.