Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya yanke jiki ya fadi a fadar shugaban kasa a lokacin da yake jawabi

A ranr Alhamis ne shugaban hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ya yanke jiki ya fadi a fadar shugaban kasa a lokacin da ya ke jawabi a wurin taron ranar Sanin kai wato National Identity Day.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Bawa dai ya fara jawabin sa kenan bai dade ba sai kawai ya fara rufe fuska da hannu yan cewa ayi hakuri ba zan iya magana ba, a zo a taimake ni, daga nan ne ministan sadarwa ya rike shi zuwa wurin zama. Sai dai kuma ko da ya zauna sai ya kasa zama ya yanke jiki ya fadi.

Daga nan sai aka taimaka masa ya fita dashi.