Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban EFCC ya yanke jiki ya faɗi a wurin taro

Shugaban hukumar EFCC Abdul-Rashid Bawa ya yanke jiki ya faɗi a yayin da yake jawabi a wurin taro a Fadar shuagban ƙasa da ke Abuja.

Jaridar Punch ta ruwaito Babban jami’in hukumar ya kanke jiki ya faɗi ne da yake gabatar da jawabi a wurin taron, inda aka ji ya yanke jawabin ya shiru, sai kuma aka ga ya yanke jiki ya faɗi.

Ministan Sadarwa, Farfesa Isah Ali Pantami ne ya riƙe shi na ɗan wani lokaci kafin a ɗauke shi a fitar da shi daga ɗakin taron.

An wallafa wannan Labari September 16, 2021 2:08 PM