GARAMBAWUL: El-Rufai ya canja wa kwamishinoni 8 wuraren aiki, harda shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Mohammed Sani

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sauya wasu kwamishinoni da wasu manyan jami’an gwamnati a kokarin da yake yi na kawo sababbin jinni a gwamnatinsa.

A sanarwar da ta fito daga fadar gwamnatin Kaduna ranar Litinin ta bayyana cikin kwamishinoni 14, an canja wa kwamishinoni takwas ma’aikatu.

Kwamishinonin da ba a taba ba sun hada da, Kwamishinan Kudi, Shari’a, Kwamishinan Gidaje da Raya Birane, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida da kuma Kwamishinan Jin Dadi da Walwalar Al’umma.

Sanarwar ta kara da cewa, Muhammad Sani Abdullahi, Shugaban Ma’aikata an sauya masa mukami zuwa Kwamishinan Ma’aikatar Kasafin Kudi.

Kwamishinonin da aka canja wa ma’aikatu sun hada da:
– Ma’aikatar Muhalli: Jafaru Sani
– Ma’aikatar Ayyuka: Thomas Gyang
– Ma’aikatar Ilimi: Halima Lawal
– Ma’aikatar Aayyukan Noma: Ibrahim Hussain
– Ma’aikatar Kananan Hukumomi: Shehu Usman Muhammed
– Ma’aikatar Kasafin Kudi: Muhammed Sani Abdullahi
– Ma’aikatar Kasuwanci, Kirkire-kire da Fasaha: Kabir Mato
– Ma’aikatar Wasanni: Idris Nyam

Sannan bayan sanya hannu a dokar kafa gundumomi a manyan biranen jihar da suka hada da Kaduna, Kafanchan da kuma Zariya, Malam Nasir ELrufai ya amince da nadin wadannan mutanen a matsayin kantomomin wadannan gundumomin:
• Balaraba Aliyu-Inuwa a matsayin kantomar gundumar Zariya
• Muhammad Hafiz Bayero a matsayin kantomar gundumar Kaduna
• Phoebe Sukai Yayi a matsayin kantomar gundumar Kafanchan

Bugu da kari, Gwamnan ya amince da canja wa wadannan:

– Umma Aboki, zuwa Babban Sakatariya a Ma’aikatar Kasafin Kudi

– Murtala Dabo zuwa Shugaban Hukumar Kula da Yadda ake Kashe Kudaden Gwamnati

– Abubakar Hassan zuwa Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya

– Tamar Nandu a matsayin Shugaban Hukumar Kasuwanni

– Khalil Nura Khalil a matsayin Shugaban Hukumar Zuba Jari da Bunkasa Kasuwanci

– Maimuna Abubakar a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Muhalli

– Amina Ladan za ta rika kula da Hukumar Kula da Hanyoyi a matsayin riko

Sannan an sanarnarwar ta kara da bayyana Farfesa Mohammed Sani a matsayin sabon shugaban Hukumar Kula da Kananan Hukumomi.

Sai kuma Muhammed Mu’azu Muqaddas a matsayin Shugaban Bayar da Agaji ta Gaggawa da Dakta Shu’aibu a matsayin babban sakatare.