SATA TA SACI SATA: Minista Malami ya kafa kwamitin binciko waɗanda ake zargi sun fara sayar da kadarorin da aka ƙwato daga hannun ɓarayin gwamnati

Ministan Shari’a Abubakar Malami ya kafa Kwamitin Bankaɗo Waɗanda Su Ka Fara Sayar Da Kadarorin Gwamnatin Tarayya, waɗanda aka ƙwato daga hannun ɓarayin gwamnati.

Kafa kwamitin ya biyo bayan ɓullar wasu rahotanni a jaridu da su ka ce wasu a cikin Ma’aikatar Harkokin Shari’a sun fara sayar da kadarorin da gwamnatin ta ƙwato a ɓoye ta ƙarƙashin ƙasa.

Cikin wata takardar da Kakakin Malami ya raba wa manema labarai a ranar Talata, ya ce, “Ministan Shari’a Abubakar Malami bai bada iznin a fara sayar da kadarorin ba. Kuma idan ma har wasu sun aikata laifin sayar da wasu daga cikin kadarorin, to ba da iznin sa ba.”

Gwandu ya ce a kan haka Malami ya kafa Kwamitin Mutum 5, da za su binciko tare da gano waɗanda ke da hannu wajen sayar da kadarorin, idan har an sayar da wasu ɗin.”

Kwamitin na ƙarƙashin shugabancin Daraktan Shigar Da Ƙararraki na Tarayya (DPP), sai kuma Babban Sakatare a Ma’aikatar Shari’a a matsayin sakataren kwamiti.

An bayar da mako ɗaya duk mai wata hujja ko ƙarin haske kan wannan zargi, to ya gaggauta aikatawa a Ofishin DPP ko Ofishin Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a, daga ranar 1 Ga Disamba zuwa 7 Ga Disamba.

“Kwamiti zai bincika ya gano idan har an fara sayar da kadarorin ta ƙarƙashin ƙasa.

“Idan ya gano an fara, to zai bankaɗo duk wani ko wasu masu hannu a cikin wannan harƙalla.

“Kadarorin da za’a yi binciken a kan su, sun haɗa da gidaje, maka-makan filaye, motocin alfarma, tankokin jiragen ruwa na ɗaukar dakon fetur, masana’antu da manyan injinan sarrafa kayayyaki a cikin masana’antun da gwamnati ta ƙwace.

Biri Ya Yi Kama Da Mutum:

Majalisar Tarayya na neman ba’asin yadda aka yi da kadarorin da aka ƙwato daga tsoffin shugabanni.

Majalisar Tarayya ta nuna damuwa dangane da rashin sanin haƙiƙanin yadda aka yi da kadarorin da aka ƙwato daga tsoffin shugabannin ƙasar nan.

Kwamitin Lura da Kadarorin Gwamnantin Tarayya ne ya bayyana haka a lokacin da Babban Sakataren Kwamitin Ƙwato Kadarorin Gwamnanti a Hannun Ɓarayin Gwamnati (PIC), Bala Samid ya bayyana a gaban kwamitin a ranar Litinin.

Shugaban Kwamitin Majalisa Honorabul Ademorin Kuye, ya bayyana cewa sun gano cewa wasu kadarorin da aka ce an sayar, to ba a sayar da su ba.

Kuma kwamiti ya gano wasu gidajen da aka sayar ɗin har yanzu ba a biya kuɗaɗen ba.

Musamman kwamitin ya nemi a kawo masa bayanai dalla-dalla dangane da yadda aka yi da kadarori ko kuɗaɗen da aka karɓo waɗanda tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha ya kimshe a ƙasashen waje, sai daga baya lokacin wannan gwamnatin aka riƙa maido kuɗaɗen.

Kuye ya kuma ɗora alamomin tambaya akan yadda aka sayar da wasu kadarorin.

Ya ce sun gano har yanzu wasu akwai jama’a a ciki, ba su fita ba, alhali an shaida masu cewa gidajen babu kowa a cikin su.

Kwamiti ya kuma nemi sanin adadin kuɗaɗen da aka sayar da kadarorin, tare da gabatar masa da shaidar ko nawa aka saka a aljihun gwamnatin tarayya.

Babban Sakataren Kwamiti Bala Samid ya ce gidajen da har yanzu mazaunan su ba su tashi ba, sun kasa biyan haya ne, kuma a duk lokacin da aka yi ƙoƙarin fitar da su, sai su je kotu su samu umarnin hana fitar da su da tsiya daga kotuna daban-daban.

Ya ce ya na maraba da duk wani mataki da Majalisar Tarayya za ta ɗauka, domin a karɓo kuɗaɗen hayar da mazauna gidan su ka ki su biya.