KATSINA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Mahara sun sake yin garkuwa da wani basarake a Katsina

Wasu gungun ‘yan bindiga sun dira garin Fankama, inda su ka yi gaba da Dagacin gari mai suna Ahmed Sa’idu da matar sa da kuma wasu mutane da dama.

Garin Fankama na cikin Ƙaramar Hukumar Faskari a jihar Katsina. Faskari ta yi iyaka da ƙaramar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Rahotanni daga yankin sun ce ‘yan bindigar ba su kashe kowa ba, amma sun shafe aƙalla sa’o’i biyu a cikin garin.

Wani ɗan uwan basaraken da aka yi garkuwa da shi mai suna Bahisullah Alhassan, ya shaida wa wakilin mu cewa an kwashe sauran iyalan basaraken waɗanda su ka raje a garin Fankama.

Ƙaramar Hukumar Faskari na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ‘yan bindiga ke addaba babu ƙaƙƙautawa.

Sace Dagacin Fankama ya da matar sa ya faru makonni biyu bayan mahara sun sako Dagacin Banye, basaraken da su ka kama bayan ya shafe kwanaki 26 a hannun su.

‘Yan bindiga sun sako Dagacin Banye, Bishir Giɗe, wanda suka kama kwanaki 26 da suka gabata.

Garin Banye ya na cikin Ƙaramar Hukumar Charanci ta Jihar Katsina.

‘Yan bindigar sun kuma sako wani yaro ɗan sakandare da suka kama tare da Bishir Giɗe.

Wani ɗan uwan dagacin da mai suna nura, ya tabbatar da kuɓutar basaraken, bayan ya ji ta bakin makusantan Bishir Giɗe daga Banye.

Sai dai kuma bai san ko nawa aka biya ba kafin a sako shi tare da ɗalibin a ranar Laraba da yamma.

Premium Times Hausa ta bada labarin yadda Mahara suka yi garkuwa da Dagacin Banye, yankin Charanci tun a tsakiyar watan Oktoba.

Wasu ‘yan bindiga ne dai suka yi tattaki cikin dare a ranar Juma’a, su ka dira Banye, inda su ka yi gaba da Maigarin Banye, Bishir Giɗe.

Banye ta na cikin Ƙaramar Hukumar Charanci, kuma ta yi iyaka da garin Barkiya ta ɓangaren Ƙaramar Hukumar Kurfi.

Wani ɗan jarida mai suna Nura Ishaq da ke Katsina, wanda ɗan uwan basaraken ne, ya tabbatar da labarin, kuma ya ƙara da cewa zuwa yanzu ba a tantance yawan waɗanda aka tafi da su ba, saboda yanke wayoyin sadarwa a cikin jihar.

Haka kuma ba a ji ɗuriyar halin da ake ciki ba tun bayan tafiya da Bishir Giɗe, saboda katse wayoyin sadarwa a wasu sassan jihar Katsina.

Kakakin Yaɗa Labaran Masarautar Katsina, ya shaida wa wakilin mu cewa ya samu labarin an yi garkuwa da Maigarin Banye, amma babu wani ƙarin haske tukunna daga jami’an tsaro zuwa ga masarautar Katsina.

Ya sanar da wakilin mu cewa da zarar ya samu rahoto, zai yi masa ƙarin haske.

Duk da ana ganin yankin Charanci babu dazuka, ana mamakin yadda aka yi tattaki a ƙasa har cikin Banye a yi garkuwa da mutane.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES Hausa cewa bayan mahara sun tafi da Bishir Giɗe, jama’a sun bi sawun su inda aka gano cewa nausawa kudu aka yi da shi, kuma a ƙasa, ba bisa babura ba.

“An bi sawun su har kusa da Rawayau, daga nan kuma aka rasa inda su ka yi.” Inji majiyar.

Watannin baya a cikin Ƙaramar Hukumar Charanci an yi garkuwa da Dagacin Radda.