HUKUNCIN KOTU KAN KORAR SARKI SANUSI II: Gwamnatin Kano ta ce za ta ɗaukaka ƙara

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ba ta gamsu da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke kan haramta korar da ta yi wa Murabus Sarki Muhammadu Sanusi ba.

Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Musa Lawan ya shaida wa jaridar Solace cewa gwamnatin Kano za ta ɗaukaka ƙara.

A ranar Talata ce Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta haramta korar da aka yi wa Sanusi, tare da umartar cewa a biya shi diyyar naira miliyan 10, saboda an tauye masa haƙƙi.

Kotun kuma ta ce Sanusi na da ‘yancin ya dawo Kano ya ci gaba da zaman idan ya na bukatar hakan. Kuma zai iya shiga Kano a duk lokacin da ya ke so.

Sannan kuma hukuncin kotu ya umarci Kano, ‘yan sanda da SSS su nemi afuwar Sanusi, ta hanyar buga neman afuwar a cikin jaridu biyu na ƙasar nan.

Sai dai kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano ya ce ai dokar Najeriya ta bada hurumin a kare martabar sarautar gargajiya.

“Al’adar sarautar gargajiya ce sama da shekaru 100 idan aka tsige sarki, to za a ɗauke shi a maida shi wani gari, a nesanta shi daga masarautar.’ Inji Kwamishinan Shari’a na Kano.

Hukuncin Kotun Tarayya:

Kotu ta haramta korar da Gwamnatin Kano ta yi wa Sarki Sanusi II, ta ce ya na da ‘yancin ya zauna a Kano.

Sannan kuma ta nemi gwamnatin Kano ta nemi afuwar Sanusi, ta hanyar buga neman afuwar a gidajen jaridu biyu.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta haramta korar da Gwamnatin Jihar Kano ta yi wa Murabus Muhammadu Sanusi II, bayan cire shi daga sarautar Kano.

A ranar Talata ce Mai Shari’a Anwuli Chikere ta haramta korar da aka yi masa zuwa Jihar Nasarawa, cewa haram ce, kuma a gaggauta biyan sa diyyar naira miliyan 10.

Chikere ta ce hukuncin da gwamnatin Kano ta ɗauka bayan tsige Sanusi cikin 2019 ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ta ce Sanusi na da ‘yancin ya ci gaba da zama a Kano, ko ya kai ziyara idan ya ga dama.

“Dokar Masarautar Kano da Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaƙaba ta 2019 kan Sarki Muhami Sanusi, haramtacciya ce. Saboda ta kauce wa kundin dokokin Najeriya.”

A kan haka kotu ta ce Hukumar ‘Yan Sanda, SSS da Gwamnatin Jihar Kano biya Muhammadu Sanusi diyyar Naira miliyan 10, saboda sun ɗauke shi zuwa Abuja da ƙarfin tsiya, daga can suka wuce da shi jihar Nassarawa.

A ranar 12 Ga Maris, 2020 Muhammadu Sanusi ya shigar da ƙarar tsuye masa haƙƙin walwala. Amma bai ɗaukaka ƙarar tsige shi da aka yi ba.