BINCIKEN ‘Pandora Papers’: An bankaɗo yadda wata mai shari’a ta sayi kamfacecen gida a Landan, bayan ta kafa kamfani a Birtaniya

‘Banza Ta Kori Wofi, Alƙali Ɗaurin Ɓarayi: Bayan Mai Shari’a Stella Ogene ta Kotun Ɗaukaka Ƙara a Kotun Gargajiya ta Jihar Delta mai arzikin ɗanyen mai ta yi ritaya a cikin watan Nuwamba, 2020, ta sha yabo da jinjina wajen shaidar aiki da gaskiya daga bakin Gwamna Ifeanyi Okowa. Har ma ya yi kira wadda ta maye gurbin Stella mai suna Patience Elumeze, cewa ta yi koyi da Stella ɗin.

Sai dai dukkan waɗanda su ka taru wurin yabon Stella bayan ta shafe shekaru 21 ta na alƙalanci, ba su san almurar ta shafe shekaru ta na damfare kuɗaɗe a asusun ƙasar waje ba.

Wannan abu da ta yi a cikin sirri kuwa babban laifi ne da ya kara dokokin Kundin Mulkin Najeriya.

Kuma ta ci amanar aikin gwamnati da ta yi rantsuwar karɓa, wanda ya haramta mata buɗe kamfani a asirce.

Ko da ya ke Stella ba a ɓoye ta yi na ta kamfanin ba. Bayanai sun nuna cewa ta yi rajista da Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Ƙasa (CAC) da sunan ta ɓaro-ɓaro tun fiye da shekaru 10 da su ka wuce.

Ba tare da ta bayyana yawan kadarorin ta ba, Stella ta fake da yin rajistar kamfani a CAC a nan Najeriya.

Domin tsallake siraɗin matambayan Ingila masu bibiyar yadda aka yi ta samu kuɗin ta, tunda ma’aikaciyar gwamnati ce, sai Stella ta nemi shawarar wani kamfanin saƙala-saƙala, domin ya yi mata kurɗa-kurɗar sayen gida a Landan, ba tare da an gano ta ba.

Mai Shari’a Stella kamar yadda PREMIUM TIMES ta binciko, ta tuntuɓi kamfanin adana sirrin harƙallar kuɗaɗe na Cook Worldwide, mai ofishi a Panama.

Cook Worldwide ya ƙware wajen ɓoye wa ɓarayin gwamnati kuɗaɗen sata a waje, bisa yarjejeniyar har ranar tashin kiyama ba za su fallasa masu kuɗin ba, ballantana a san su. Kuma dama kamfanin na wani ruwa-biyu ne, haifaffen Birtaniya, amma iyayen sa ‘yan asalin Najeriya ne, mai suna Obianaba Chike. Ya na hada-hadar dillancin gidaje a Landan.

Cook Worldwide ya kafa wa Stella kamfani mai suna Assete Media Limited, a ranar 7 Ga Satumba, 2009. Kuma Shella ɗin ce babbar darakta ta kamfanin. Haka takardun da ke hannun PREMIUM TIMES su ka tabbatar.

PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Stella, amma sai ta ƙaryata, ta ce babu ruwan ta da wannan kamfani, wanda ke da alaƙa da kamfanin mai na Shell.

Amma yayin da aka tura mata kwafe-kwafen takardun bayanan da ke nuna tabbas kamfanin na ta ne, kuma har da sa hannun ta, sai ta ce ita hannun jari kaɗai gare ta a kamfanin, ba na ta ba ne.

An sake aika mata kwafen takardun da ke nuna cewa Assete Media na ta ne, amma daga ranar har yau ba ta ƙara cewa komai ba.

Watanni kaɗan bayan kafa kamfani, sai Stella ta sayi tamfatsetsen gida a Landan da sunan Assete Media Limited.

Gidan wanda ta saya a kan fam 224,000 (kwatankwacin naira miliyan 43), ya na kan titin Old Registry Garden, HA8 7LS.