Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta ɗauki alhakin buɗe wa fararen hula wuta a Ƙauyen Buhari, Jihar Yobe

A ƙarshe dai Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta bayyana cewa ita ke da alhakin kai hari ta sama da jirgin yaƙi, a Ƙauyen Buhari, wanda ke cikin Ƙaramar Hukumar Yunusari a Jihar Yobe.

Harin wanda aka kai a ranar Laraba, an ce ya yi sanadiyyar kashe mutum 10 tare da jikkata mutum sama da 20.

Majiyoyi daga cikin yankin dai sun ce Sojojin Saman Jamhuriyar Nijar ne su ka kai harin wurin ƙoƙarin fatattakar wasu ‘yan Boko Haram.

Da farko kuma Rundunar Sojojin Saman Najeriya ta nesanta kan ta da kai harin wanda aka buɗe wa fararen hula wuta a ƙwauyen.

“Ƙarya ake mana, ba Sojojin Saman Najeriya su ka kai harin ba. Rabon da Sojojin Sama su yi wani farmaki a Yobe tun a ranar 5 Ga Satumba, 2021.” Haka Kakakin Rundunar Sojojin Saman Najeriya, Edward Gabkwet ya bayyana a ranar Laraba

Sai dai kuma sa’o’i 24 daga baya, Rundunar Sojojin Saman ta yi amai ta lashe, inda ta fito ta bayyana cewa Sojojin Saman Najeriya ne su ka kai farmakin a bisa kuskure, kamar yadda Gabkwet ɗin ya sake bayyanawa daga baya.

Ya ce lamarin ya faru ne bayan da su ka samu rahoton gilmawar wasu ‘yan Boko Haram a kan gaɓar Kogin Kamadougou.

“Daga nan Sojojin Saman Najeriya su ka rufa su a kan iyakar Najeriya da Nijar a ranar 15 Ga Satumba, 2021.

Sanarwar ta ce an kashe fararen hula a kan kuskure ne.

Idan ba a manta ba, shekaru uku da su ka wuce, Sojojin Saman Najeriya sun yi ruwan wuta daga a kan Sansanin ‘Yan Gudun Hijira a Rann, cikin Jihar Barno, inda su kashe sama da mutum 260.

A wannan karo kuma, bayan Rundunar Sojojin Najeriya ta nesanta kan ta da kai farmakin a Yunusari, Premium Times ta bada labarin yadda Sojojin Jamhuriyar Nijar su ka afka wa mutanen ƙauyen Buhari da kisa bisa kuskure a Jihar Yobe.

An tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 10 tare da jikkata wasu mutum 20 a harin da Sojojin Jamhuriyar Nijar su ka kai wa ƙauyen Buhari.

Ƙauyen Buhari dai wani gari ne da ke da tazarar kilomita 20 daga Kananmma, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Yunusari ta Jihar Yobe.

Lamarin ya faru ne yayin da rahotanni su ka ce Sojojin Nijar sun afka garin ne lokacin da su ke farautar wasu ‘yan Boko Haram.

An kai harin ne jirgin yaƙi, inda aka kashe mutane da kuma jikkata wasu.

Ƙaramar Hukumar Yunusari na kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Ganau ya ce da idon sa ya ga motoci uku ƙirar Toyota Hilux ɗauke da waɗanda aka ji wa rauni an shiga da su Babban Asibitin Geidam.

Wata majiya kuma ta tabbatar da cewa an garzaya da wasu Babban Asibitin Gashua.

Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da lamarin, kuma yanzu haka Sojojin Najeriya sun kewaye garin, sun hana jami’an tsaro shiga, cikin waɗanda aka hana ɗin kuwa har da ‘yan sanda.

Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Yobe, Dungus Abdulkarim ya ce ba su da cikakken bayanin haƙiƙanin abin da ya faru a zuwa lokacin da aka tuntuɓe shi.

A na sa ɓangaren, Gwamnan Yobe Mai Mala-Buni ya umarci asibitocin Geidam, Gashua da Damaturu su kula da lafiyar waɗanda aka jikkata a farmakin Ƙauyen Buhari kyauta.

Haka nan kuma ya umarci Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe ta gaggauta tura kayan tallafi ga jama’ar ƙauyen da abin ya shafa.

Sannan kuma ya bada umarnin jami’an gwamnati su yi aiki tare da jami’an sojoji domin a gano musabbabin farmakin.

Buni ya miƙa ta’aziyya da jaje da alhini dangane da wannan mummunan hari.