Sanatan APC ya koka da yawan tulin bashin da Buhari ke ciwowa, da yadda Majalisa ke gaggawar amince masa

Sanata Ali Ndume daga Jihar Barno ya nuna matuƙar damuwa ganin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke giringiɗishin yawan ciwo bashi.

Ndume ya kuma nuna damuwa ganin yadda Majalisar Dattawa a koda yaushe ta ke rawar-jikin amincewa da dukkan buƙatu da dalilan ciwo bashin da Buhari ke gabatarwa a Majalisa.

Sanatan ya ce abin haushi da takaici, har yanzu babu wasu muhimman ayyukan raya ƙasa birjik a ƙasa da za a iya tinƙaho da su, waɗanda za a ce an gina su ne daga cikin maƙudan kuɗaɗen bashin da ake ciwowa.

Ndume ya yi wannan tsokaci a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, a Abuja.

Sanatan ya na magana ne dangane da bashin da Buhari ya aiko neman amincewar Majalisar Dattawa domin ya ciwo, waɗanda kuɗaɗen a yanzu za su iya kai naira tiriliyan 2.2. Kuma dama ana bin Najeriya bashin Naira tiriliyan 33.

Yayin da PDP ke cewa bashin da Buhari zai ƙara ciwowa zai ƙara burma ‘yan Najeriya cikin ƙuncin rayuwa, APC kuwa cewa ta ke yi bashin “alheri zai zama ga ƙasar nan. Da kuma inganta rayuwar ‘yan ƙasar su kan su.

“Ni ba masanin kuɗaɗe ba ne. Amma batun gaskiya ba karɓo bashin ne matsala ba. Inda matsalar ta ke shi ne abin da za a yi da kuɗaɗen da kuma yadda za a riƙa kulawa da su.”

Ndume ya ce akwai basussukan da na tilas ne, akwai kuma waɗanda ake ciwowa haka kawai don giringiɗishi.

“Akwai ƙarancin kayayyakin inganta rayuwa a faɗin ƙasar nan. To kuma mu na jin nan a Abuja da kuma a bakin sauran jama’a cewa idan aka fitar da kuɗaɗe, sai a rasa abin da ake yi da su. Domin babu wani abin a zo a gani da za a iya shaidawa.”

Haka nan kuma Ndume ya nuna ɓacin rai ganin yadda idanun Majalisar Dattawa ke rufewa su riƙa gaggawar amincewa da dukkan buƙatun ciwo bashi da Buhari ke aika masu neman amincewar su.

Farkon watan Agusta Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe na Majalisar Tarayya ya nuna damuwa kan tulin bashin da Najeriya ke ciwowa.

Sai dai kuma a cikin makon da ya yi ƙorafin ne, sai Ministar Harkokin Kuɗaɗe ta ce tulin bashin ba mai kumbura ciki ba n.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ta bayyana cewa har yanzu bashin da Najeriya ke ciwowa bai kumbura mata cikin da zai iya fashewa ba.

Ministar ta ce har yanzu Najeriya ba ta tsallake ƙa’idar Gejin Tattalin Arzikin Cikin Gida na ba, inda ta ce har yanzu bashin bai wuce kashi 23 bisa 100 ba.

Zainab ta yi wannan bayani ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin.