Lokaci muke jira mu fallasa masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa wato EFCC Abdulrasheed Bawa, ya ce nan bada jimawa ba kowa zai san sunayen masu ɗauakar nauyin ta’addanci a Najeriya, lokacin da ya dace kawai suke jira.

Yana magana ne yayin wani shirin siyasa na tashar talabijin ta Channels jiya Alhamis.

  • Lokaci muke jira mu fallasa masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya
  • Ana murna da mutuwar wani matashi da ya mutu wurin satar wayar wuta a Potiskum

Bawa, wanda ya faɗi lokacin da yake jawabi a fadar shugaban kasar a jiyan, ya ce likitoci sun shaida masa cewa bashi da wata matsala, don haka a yanzu ya murmure.

”Makoshi na ne ya dan bushe, sai likitoci suka bukaci in sha ruwa sosai, daga baya kuma na wartsake ba wata matsala yanzu” inji shi.

An wallafa wannan Labari September 17, 2021 12:53 PM