RIKICIN PDP: Ayu ya musanta karɓar harƙallar naira biliyan 1, ya yarda ya karɓo miliyan 100 hannun wani gwamna

Makonni uku bayan Gwamna Nyesom Wike na Ribas ya zargi Shugaban PDP, Iyorchia Ayu da tarɓar kuɗaɗe, a karon farko Ayu ya fito ya ce bai karɓa ba.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Tiwita, ya ce “ban taɓa karɓar naira bilyan 1 a hannun wani a Legas ba.
Baya ga wannan zargi dai, Wike ya zargi Ayu da raba wa wasu shugabannin PDP naira miliyan 120 domin su goyi bayan kada ya sauka daga shugabancin PDP.
A ranar Juma’a kuma Wike ya zargi Ayu da karɓar kuɗin wata kwangila ta naira miliyan 100, wadda Wike ya ce an biya Ayu kuɗin sau biyu.
A martanin sa, Ayu ya ce abin da ya sa bai yi magana tun tuni ba, saboda ya na gudun kada bayanan sa su ci karo da wasu bayanan. Kuma ana ta ƙoƙarin ganin an samu sulhu a PDP.
“Amma na fito ne yanzu na yi magana saboda na ga abin har ya kai ga ana ci min mutunci, kuma ana ci wa ‘ya’ya na mutunci.”
Idan ba a manta ba, Wike ya ce “idan ci gaba da fallasa harƙallar Ayu, to ‘ya’yan sa ma sai sun yi da-na-sanin haihuwar su da ya yi.”
Ayu ce bai karɓi kuɗin kowa a Legas ba kamar yadda Wike ya yi zargin ya karɓa.
“Abin da ya faru, lokacin da na zama shugaban PDP, jam”iyyar ba ta da kuɗi. Sai Atiku ya bayar da shawara a nemi ramce a wani banki mallakar wani tsohon ɗan PDP, wanda a yanzu ba ya cikin jam’iyyar.
“Amma daga baya sai mu ka canja shawara, ba mu nemi ramcen ba ma, ballanata kuma a ce mun karɓa,” inji Ayu.
Batun zargin karɓar kuɗaɗen kwangila ɗaya sau biyu kuwa, ita ma Ayu ya ce ƙarya ce.
“Tabbas wani gwamna ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100, wadda aka yi amfani da ita a aikin Cibiyar PDP. Amma ni daga ita ban sake karɓar wata naira miliyan 100 daga Kwamitin Zartaswar PDP ba.”