Masu maular ‘kudaden kama haya’ a hannun Ayu ke hana sasanta rikicin PDP -Wike

Gwamna Nyesom Wike ya bayyana cewa wasu manyan ‘yan maular kuɗaɗen haya daga PDP ne ke hana ƙoƙarin da shi Wike ɗin ke yi domin a ɗinke ɓarakar da ke cikin jam’iyyar a cikin ruwan sanyi.
Wike da wasu gwamnonin PDP huɗu dai su na so Shugaban PDP Iyorchia Ayu ya sauka, a zaɓi ɗan kudu ya riƙe shugabancin jam’iyyar.
Wike ya yi zargin masu hana ruwa gudu a PDP ɗin, lokacin da ɗan takarar gwamnan Jihar Kuros Riba na PDP, Sandy Onor ya kai masa ziyara tare da wasu magoya bayan jam’iyyar.
Wike ya ce rikicin PDP ya ƙara muni ne haka kawai, saboda wasu marasa kishin jam”iyya da ya kira “kuraye da masu maular kuɗaɗen kama haya,” sun ƙi bari a wanzar da gaskiya, adalci da daidaito a cikin PDP.
Ya ce ba zai taɓa goyon bayan tafiyar PDP a yanzu ba, inda shugaban jam’iyya daga Arewa, ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewa sannan kuma Darakta Janar na Kamfen shi ma daga Arewa.
Ya ce munaficci ne kawai PDP ke yi da ta ke sukar takarar Muslim-Muslim a APC, alhali ita kuma ta ɗaure gindin wani yanki na ƙasar nan ya ƙara ci gaba da shugabanci na wasu shekaru takwas.
Ya ce idan har ana son zaman lafiya a cikin PDP, to tilas sai jam”iyyar ta bi tsarin da dokokin ta su ka gindaya.
“Shugaban Jam’iyya ya ce idan har ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito daga Arewa, to shi Ayu zai sauka daga shugabanci, tunda shi ma ɗan Arewa ɗin ne.
“To yanzu ɗan Arewa ɗin ne ɗan takara. Ya sauka mana. Shi kuma ya ce “ba zan sauka ba.” Mutane kuma na ce masa ya je ya sa labule shi da Wike.
“Na yarda da takarar Atiku, na kuma yarda da takarar mataimakin takarar Atiku. To sai me kuma?
“Tun da ni na janye waccan jayayya tawa, kai ma ka cika na ka alƙawarin mana. A bai wa kudu muƙami ni fa shi ne kawai jayayya ta a yanzu.
“Amma bai yiwuwa a ce yanki ɗaya ke da ɗan takarar shugaban ƙasa, shugaban jam’iyya da kuma Darakta Janar na kamfen.” Cewar Wike.
Ya ce kowa ya san an yi wa Kudu rashin adalci, amma kuma an rufe ido an ƙi magana.
Ya ce PDP za ta ƙara ruftawa cikin rikici muddin ba a bai wa kudu shugabancin jam’iyya ba.
Ya ce za su ci gaba da neman a bai wa kudu shugabancin jam’iyya har sai an yi adalci an biya masu buƙatar su.