Kotu ta wanke Nnamdi Kanu daga shari’ar Kamo shi daga Kenya, amma ba ta wanke shi daga tuhumar tserewa bayan beli ba – Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta maida raddi da kuma ƙarin haske dangane da sallamar da ake cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi wa ɗan tawaye Nnamdi Kanu.
Kwana ɗaya bayan kotu ta kori tuhumar da ake yi wa Kanu, wanda ya ɗaukaka ƙara a can, inda kotu a ce an kamo shi ba bisa ƙa’ida ba, ita kuma gwamnatin tarayya ta ce ai kotu ba ta sallami Kanu a tuhumar tsallake beli da ya yi lokacin da ya gudu daga ƙasar nan ba.
Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Maigari Dingyaɗi, ya ce gwamnati na ci gaba da nazarin hukuncin da kotu ta yanke kafin ta ɗauki mataki na gaba.
Haka shi ma Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami ya ƙara jaddadawa, a cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran sa, Umar Gwandu ya fitar tare da sa hannun sa a ranar Alhamis.
Dingyaɗi ya ce kotu ta kori ƙarar da Kanu ya ɗaukaka inda ta ce a sallame shi, to amma fa ba ta ce ya fita daga sauran tuhumar da ake yi masa ba.
Kanu Shugaban IPOB, wanda ya ke ɗan Najeriya ne kuma ɗan Birtaniya, ya na tsare ne a hannun SSS bisa zargin sa da ta’addanci, tun bayan da aka cumuimuyo shi daga Kenya, cikin watan Yuni, 2021.
Bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce a sake shi, Dingyaɗi ya ce gwamnati na nazarin lamarin.
Kotu ta wanke Nnamdi Kanu daga shari’ar Kamo shi daga Kenya, amma ba ta wanke shi daga tuhumar tserewa bayan beli ba.
Gwamnatin Najeriya ta maida raddi da kuma ƙarin haske dangane da sallamar da ake cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi wa ɗan tawaye Nnamdi Kanu.
Kwana ɗaya bayan kotu ta kori tuhumar da ake yi wa Kanu, wanda ya ɗaukaka ƙara a can, inda kotu a ce an kamo shi ba bisa ƙa’ida ba, ita kuma gwamnatin tarayya ta ce ai kotu ba ta sallami Kanu a tuhumar tsallake beli da ya yi lokacin da ya gudu daga ƙasar nan ba.
Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Maigari Dingyaɗi, ya ce gwamnati na ci gaba da nazarin hukuncin da kotu ta yanke kafin ta ɗauki mataki na gaba.
Haka shi ma Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami ya ƙara jaddadawa, a cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran sa, Umar Gwandu ya fitar tare da sa hannun sa a ranar Alhamis.
Dingyaɗi ya ce kotu ta kori ƙarar da Kanu ya ɗaukaka inda ta ce a sallame shi, to amma fa ba ta ce ya fita daga sauran tuhumar da ake yi masa ba.
Kanu Shugaban IPOB, wanda ya ke ɗan Najeriya ne kuma ɗan Birtaniya, ya na tsare ne a hannun SSS bisa zargin sa da ta’addanci, tun bayan da aka cumuimuyo shi daga Kenya, cikin watan Yuni, 2021.
Bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce a sake shi, Dingyaɗi ya ce gwamnati na nazarin lamarin.
Kanu ya arce daga beli ne bayan Sanata Nnanya Abaribe ya karɓe shi beli, lamarin da ya nemi jefa Abaribe cikin tsomomuwa.
Dama jama’a da dama na ganin cewa zai yi wahala gwamnatin Najeriya ta saki Kanu, idan aka yi la’akari da cewa a cikin 2017 Mai Shari’a Binta Nyako ta bayar da belin sa bayan kama shi cikin 2015, amma aka ƙi sakin sa.