RIKICIN BILLIRI: An kashe mutum bakwai, an lalata shaguna 401, gidaje 41, wuraren ibada 33 – Kwamitin Tantance Barna

Kwamitin Tantance Yawan Barnar Rikicin Billiri a Jihar Gombe, ya bayyana cewa an kashe mutum bakwai, an kone shaguna 401, gidaje 41 da wuraren ibada 33.

Shugaban Kwamiti kuma Kwamishinan Tsaro na Jihar Gombe, Adamu Dishi ne ya bayyana haka a lokacin da kwamiti ke damƙa wa Gwamna Inuwa Yahaya rahoton binciken.

Wannan mummunan rikici dai ya faru a watan Fabrairu, 2021, bayan da ƙabilun yankin Billiri su ka fusata da jinkirin bayyana sabon Sarkin Tangale, wato Mai Tangale, bayan mutuwar Audu Buba-Maisheru.

Da ya ke karbar rahoton, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce zai yi amfani da shawarwarin da kwamitin ya bayar.

Daga nan ya ce ya kamata al’umma su zauna da juna lafiya, domin babu wani kuɗi da zai iya maye gurbin ran da aka kashe.

PREMIUM TIMES ta buga labarin sabon rikicin da ya sake barkewa a Gombe, wanda ya ci ran mutum ɗaya, aka ƙone gidaje 50.

Sabon Rikici Kan Gona:

An kashe mutum ɗaya, an ƙonagidaje 50 tsakanin ƙabilun Shongkm da Filiya a Gombe.

Aƙalla mutum ɗaya aka kashe, sannan aka ƙona gidaje sama da 50 a wani mummunan rikicin gona da ya barke tsakanin ƙabilun yankin gundumar Shongom da na Filiya, a Jihar Gombe.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Gombe, Julius Ishaya ne ya bayyana haka bayan fitowa daga taron Majalisar Tsaro ta Jihar Gombe.

Ya ce rikicin ya barke ne tun a ranar Asabar, inda aka kashe wata mata ɗaya kuma aka banka wa gidajen a
kimanin 50 wuta.

An ɗibga asarar kayan abinci, kayan masarufi da sauran kayyyakin amfani na yau da kullum.

Ya ce Gwamnatin Jihar Gombe ta yi tir da tashin hankalin, kuma ta gargaɗi al’ummobin bangarorin biyu su rungumi zaman lafiya da juna.

“Sannan kuma Gsamnatin Jihar Gombe ta umarci Mai Kaltungo, Sale Mohammed ya shiga tsakani domin a sasanta kuma raba rikicin tare da shiga tsakani.

“Majalisar Tsaron Jihar Gombe na ƙara jaddada cewa har yanzu dokar haramta ƙungiyoyin banga da na farauta na nan ba a cire ta ba. Kuma an umarci jami’an tsaro su yi maganin waɗanda su ka karya wannan dokar.” Inji shi.

Ya ƙara da cewa an umarci shugabannin bangarorin ƙabilun biyu su zauna da matasan yankunan su domin a tabbatar da an kauce wa sake afkuwa da kuma ƙara bazuwar rikicin a wasu yankuna.

Kwamishinan Tsaro na Jihar Gombe, Adamu Dishi, ya ce tuni zaman lafiya ya dawo a yankunan.

“An kuma umarci jami’an tsaro su zaƙulo tare da damƙe duk wani mai hannu a barkewar rikicin, domin a hukunta shi.”