Shugabannin Hukumar NSITF da Buhari ya tsige, za su amayar da naira miliyan 181, cikin su har da Jasper Azuatalam

Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige shugabannin Hukumar NSTIF tun daga Manajan Darakta, Bayo Somefun da sauran wasu manyan jami’ai 12.

A cikin su har da Jasper Azuatalem, wato Daraktan Gudanarwa, wanda kafin samun aiki a NSTIF, ya yi suna sosai wajen kamfen din zagin PDP, ya na kiran ‘yan jam’iyyar barayi.

Buhari ya tsige su ne saboda an gano sun rika antaya makudan kudade su na dorawa a kan hakikanin adadin kudin kwangiloli su na karkatar da kudaden cikin aljihun su.

Tun da farko dai dakatar da su Buhari ya fara yi har sai yadda hali ya yi, sannan kuma ya sa aka nada masu kwamitin bincike.

Tsigewar da Shugaba Buhari ya yi masu za ta fara ne daga ranar 1 Ga Yuli, 2021. Sannan kuma an maye gurbin Somefun da Micheal Akabogu, tsohon Mataimakin Shugaban Bank of America (BoA).

Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Kwadago ta Tarayya, Charles Akpan ya fitar, ya ce Shugaba Buhari ya amince da korar sauran Manyan Daraktocin NSITF su uku, Tijjani Sulaiman, Jasper Azuatalem DA Olukemi Nelson.

Somefun da sauran wadannan manyan daraktoci uku, za su amayar da naira miliyan 181.56, wadanda su ka wawura ta haramtacciyar hanya, kuma su ka dagargaje kudaden wajen bushasha da tafiya hutu kasashen waje, da sauran hanyoyin da Hukumar Tantance Albashi da Alawus din Ma’aikata ba ta amince a kashe kudaden ba.

An kuma tsige sauran manyan jami’an hukumar ta NSTIF su tara, tare da maye gurbin su da wasu.

Buhari ya bada umarnin cewa duk wani jami’i ko kamfanin da aka umarta ya maido kudade, idan bai maido ba to a gaggauta damka shi ga hukumar EFCC ko ICPC, domin su taka ruwan cikin sa, ya amayar da kudaden.