Korona ta kashe mutum 28 a Najeriya ranar Litinin – NCDC

Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa, NCDC ta bayyana cewa korona ta kashe mutum 28 a ranar Litinin da ta gabata.

NCDC ta buga adadin yawan mutanen 2
su 28 a shafin ta na Twitter cikin dare a ranar Litinin.

Wannan ne adadi mafi yawa na kisan rana ɗaya da korona ta yi a ƙasar nan, tun farkon bullar cutar a Najeriya cikin watan Fabrairu, 2020.

A baya an taba samun mutuwar mutum 27 a rana ɗaya, a ranar 30 Ga Janairu, 2021, wanda shi ne adadi mafi yawa kafin alƙaluman mutum 28 da su ka mutu a ranar Litinin.

Alƙaluman ranar Litinin sun nuna cewa korona ta kama mutum 166,518 jimla kenan, amma sama da 150,000 sun warke.

Mutuwar mutum 28 a ranar Juma’a ta haddasa fargaba a zukatan hukumar NCDC da ‘yan Najeriya da dama, ganin cewa adadin ya zo daudai lokacin da gwamnatin Najeriya ke farautar sama da mutum 200, wadanda su ka shugo ƙasar nan, amma su ka sulale ba tare da tsayawa an kullace su ba.

Zuwa yanzu dai mutum miliyan ɗaya kacal aka yi wa rigakafin korona a Najeriya, ƙasa mai yawan jama’a kusan miliyan 200.

Matsalolin da ƙasar ke fuskanta wajen yaƙi da korona, sun haɗa har da rashin yarda akwai cutar a Najeriya da wasu ke nunawa.

Da yawan mutane na zargin jami’an gwamnati da mahukunta su na zuguguta cutar ne domin a samu kafar karkatar da maƙudan kuɗaɗe kawai.

Zargin yadda riƙa karkatar da kuɗaɗe da kayan abincin tallafin korona ya ƙara sa jama’a da dama ba su bai wa gwamnati goyon baya wajen shirin daƙile cutar korona a Najeriya.