Rikici tsakanin Hausawa da Fulanin Ondo ya yi sanadiyyar ran wani mutum daya

A sanadiyyar rikici da ya barke tsakanin Hausawa ‘yan kasuwa da wasu Fulani da ke jihar Ondo yayi sanadiyyar ran wani mutum daya.
Majiya ta shaida cewa rikicin ya barke ne tsakanin Hausawa ‘yan Kasuwa da Fulani dake harkokin kasuwancin su a wuri daya da a wannan kasuwar.
An fara gwabzawa ne tun a daren Talata ya kai har safiyar Laraba ana balla tsakanin abokan zaman biyu. Dukkan su dai sun yi asarar dukiyoyin su a wannan kasuwa da suke sana’ar cinikayyar su.
Rundunar ‘yan sandan jihar sun ce zaman lafiya ya dawo kasuwar, sai dai dukkan su bangarorin biyu sun tafka asaera masu yawan gaske.