KWALARA: Mutum 9 sun rasu a jihar Ebonyi

Akalla mutum 9 sun mutu sannan wasu da dama na kwance a asibitoci bayan sun kamu da cutar kwalara.

Cutar ta barke ne a kauyen Akpoha dake karamar hukumar Afikpo ta Arewa jihar Ebonyi.

Zuwa yanzu gwamnati ta ce mutum 30 ne suka kamu da cutar amma mazaunan kauyen sun ce yawan mutanen da suka kamu da cutar ya dara haka.

Gwamnati ta aiko jami’an lafiya domin dakile yaduwar cutar.

Bayan haka Shugaban karamar hukumar Afikpo ta Arewa Uchenna Ibiam ya hori mutanen karamar hukumar da su Yi amfani da duk sharuɗɗan da jami’an lafiyan za su basu domin kare kansu daga kamuwa da cutar.

Ibiam ya Kuma ce zai haka rijiyar burtsatse guda hudu a cikin makonni hudu a karamar hukumar domin ganin mutane sun samu ruwa mai tsafta.

Bayan ya ziyarci mutanen da suka kamu da cutar a asibiti Ibiam ya bada katifu, omo da kudi wa mutanen kauyen.

Daga nan wani kwararren jami’in kiwon lafiya da baya so a fadi sunnan sa saboda rashin samun izinin yin magana da manema labarai ya ce yin bahaya a waje da rashin tsaftacen ruwa na daga cikin dalilan da ya sa cutar ta barke.

Ya kira ga gwamnati da ta samar wa mazauna karkara ruwa mai tsafta, gina wa mutanen dakunan bahaya sannan ta wayar da su illan yin bahaya a waje.

Idan ba a manta ba makoni uku da suka gabata cutar ta Yi ajalin mutum biyar a kauyen Ezillo dake karamar hukumar Ishielu a jihar Ebonyi.

Ga abubuwa 10 dake haddasa barkewar cutar Kwalera

1. Rashin tsafta da barin ƙazanta a gida, musamman abinci da kayan abinci ko kwanukan cin abinci.

2. Zubar da tulin shara da bola aikin unguwanni, wadda ruwan sama ke maida ƙazantar ta s cikin jama’a.

3. Zubar da shara ko bola ko bayan gida a cikin ƙaramu da magudanan ruwa.

4. Yin bayan gida a fili ko a kan bola.

5. Rashin ruwa mai tsafta a cikin al’umma.

6. Ƙarancin asibitocin kula da marasa lafiya a cikin jama’a marasa galihu.

7. Ƙaranci ko rashin magungunan da za a bai wa mai cutar kwalara cikin gaggawa.

8. Matsalar ƙarancin jami’an kiwon lafiya a cikin jama’a.

9. Rashin hanyoyi masu kyau da za a garzaya asibiti da mai cutar amai da gudawa cikin gaggawa.

10. Shan ruwan ƙarama ko kogi, wanda ake zubar da shara, kashin dabbobi da kuma bayan gida.