Obasanjo ‘ba dattijon arziki ba ne’ – Martanin Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa irin kakkausar sukar da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ke wa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ba wani abu ba ne sai nifaƙa, son rai da ganin-ƙyashi da kuma ɓacin ran da ya ke kwana da tashi da shi a cikin zuciyar sa.
Fadar ta ce halayyar da tsohon shugaban ke nunawa kan Buhari, hali ne na dattijon da ba shi da dattako a zuciyar sa.
Haka dai Fadar Shugaban Ƙasa ta yi wa Obasanjo wannan raddi a cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya sa wa hannu a ranar Litinin.
Garba Shehu ya yi wannan raddi ne dangane da wasiƙar da Obasanjo ya rubuta a ranar 31 Ga Disamba, 2022, inda a cikin wasiƙar ya nuna goyon bayan sa ga takarar Peter Obi, wanda ke takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar LP.
Wannan goyon baya da Obasanjo ya nuna wa Obi, ya janyo mayar masa raddi daga APC da PDP, sai kuma na baya-bayan nan shi ne wannan da Fadar Shugaban Ƙasa ta yi masa.
Ba goyon bayan Peter Obi kaɗai Obasanjo ya yi a cikin wasiƙar ta sa ba, abin da ya janyo har Fadar Shugaban Ƙasa ta yi masa raddi, saboda ya ce shekaru bakwai da rabi na mulkin Buhari sun zama alaƙaƙai ga ‘yan Najeriya.
Obasanjo cewa ya yi mulkin Buhari ya kasance wa ‘yan Najeriya tamkar “wanda ya yi tsalle ne daga kaskon suya ya faɗa cikin wuta. Saboda wannan mulki ya zama tamkar rayuwar jahannama ce a duniya.” Inji Obasanjo.
‘Wai Maras Tarbiyya Ke Cewa Wani Ba Shi Da Ɗa’a’ – Shaguɓen Fadar Shugaban Ƙasa Ga Obasanjo:
Garba Shehu a cikin martanin da ya yi wa Obasanjo, ya ce “ai dama ba yanzu farau ga Obasanjo ba, saboda duk shugaban ƙasar da ya zo bayan sa, idan ya ƙi zama ɗan-amshin-shatan Obasanjo, to zai ce mulkin sa rayuwa ce irin ta jahannama.
“Kenan shi ne ke ɗanɗana rayuwar jahannamar da ya ke ta misaltawa, saboda haushin duk shugaban ƙasar da aka yi bayan sa, matsawar a yi yarda ya zama ɗan-amshin-Shata ga Obasanjo ɗin.
Yayin da Garba Shehu ya riƙa bayyana irin nasarorin da Buhari ya yi a mulkin sa, a gefe ɗaya kuma ya riƙa bayyana irin yadda Obasanjo ya riƙa yi wa dimokraɗiyya rugu-rugu, inda ya riƙa ɗaure wa ‘yan majalisar dokokin jihohi gindi su na tsige gwamnoni a lokacin mulkin sa, ta haramtacciyar hanya.
Ya bada misalan gwamnonin da Obasanjo ya sa aka tsige tsakanin 1999 zuwa 2007, da su ka haɗa da Joshua Dariye na Filato, Peter Obi, Chris Ngige da Ayo Fayose na Ekiti.
Sannan kuma Shehu ya tunatar da jama’a irin yadda a zamanin mulkin sa, Obasanjo ya riƙe wa Jihar Legas kason kuɗaɗen ta da tarayya ke ba ta, saboda ‘yar tsamar da ke tsakanin sa da gwamnan lokacin, Bola Tinubu.
Bayan nan, Garba ya tunatar da Obasanjo irin yadda gwamnatin sa ta riƙa ɗaure wa cin hanci da rashawa tare da karya tattali gindi a ƙasar nan.
An tuna masa yadda ya riƙa yin gwanjon kadarorin gwamnatin tarayya a arha ɓagas.
Kamfanonin da Obasanjo ya sayar a lokacin sun haɗa da kamfanin alminiyan na ALSCON, wanda aka gina kan dala biliyan 3.2, amma Obasanjo ya sayar da shi dala miliyan 130 kacal.
Sauran su ne kamfanin Sarrafa Ƙarara na Delta Steel, wanda aka kafa cikin 2005, wanda ya ci dala biliyan 1.5, amma aka sayar da shi dala miliyan 30’ga kamfanin Global Infrastructure da kuma wasu dama.