RASHIN TSARO: Boko Haram sun tada bama-bamai da nakiyoyi sau 1,366 a Barno, Adamawa da Yobe cikin shekaru biyar -UN

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa a cikin shekaru biyar Boko Haram sun tayar da bama-bamai da nakiyoyi har sau 1,366 a jihohin Adamawa, Barno da Yobe na Arewacin Najeriya.

Wasu daga cikin tarwatsewar bama-baman sun faru ne daga tashin nakiyoyi da butsa-butsan na’urorin tashin wuta idan an kunna su.

Kodinatan Majalisar Ɗinkin Duniya mai lura da Ayyukan Agaji da Jinƙai a Najeriya, Edward Kallon ne ya bayyana waɗannan adadin tashin bama-bamai a jihohin uku, a lokacin da ya ke jawabi a wani taron Sanin Makamar Aiki a Abuja, a ranar Alhamis.

Rahoton ya kuma nuna cewa jihar Barno ce tashin bama-baman ya fi shafa, kuma ya fi yi wa mummunar illa.

“Kusan kashi 75% bisa 100% na Ƙananan Hukumomin Jihar Barno, duk sun sha fama da tashin bama-bamai da nakiyoyi.

“A Jihar Adamawa da Yobe kuma kashi 52% bisa 100% na Ƙananan Hukumomi duk sun yi fama da tashin bama-bamai.

“Saboda haka a BAY(Barno, Adamawa da Yobe, Sashin Kula da Tashin Nakiyoyi ya ƙididdige tashin nakiya har sau 1,365 tsakanin ransr 1 Ga Janairu, 2016, zuwa 30 Ga Afrilu, 2021.” Cewar rahoton.

Nakiyar Kisan Rayukan Jama’a:

Rahoton UN ya ce nakiya ta halaka mutum 129 a cikin 2020. A cikin shekarar an rasa s
rayuka 422 jimlar rayukan fararen hula da waɗanda ba fararen hula ba.”

Kallon ya ce tashin nakiya da bama-bamai ya kasance abu mai barazana a rayuwar jama’a.