RANAR MUHALLI TA DUNIYA: Gwamnatin Kaduna za ta shuka itatuwa miliyan 1.2 a jihar

Gwamnatin jihar Kaduna za ta shuka itatuwa miliyan 1.2 domin rage matsalolin canjin yanayi a jihar.

Kwamishinan muhalli da albarkun kasa Ibrahim Husseini ya fadi haka a taron shuka itatuwan da aka yi a Kaduna ranar Juma’a.

Husseini ya ce shuka itatuwa hanya ce dake inganta muhalli da kiwon lafiyar mutane.

Ya yi kira ga mutane da su rika tsaftace muhallin su tare da kiyaye sare titatuwa a wuraren su.

Husseini ya ce gwamnati za ta yi amfani da gidajen jaridu domin yawayar da kan mutane sanin mahimmancin inganta muhallinsu ta hanyar shuka tatatuwa.

Bayan haka shugaban hukumar tsaftace muhalli ta jihar Kaduna Lawal Jibrin KEPA ya ce hukumar za ta dauki nauyin kula da itatuwan da aka shuka domin su girma da kyau.

Jibrin ya yi kira ga mutane da su rika zubar da shara a wuraren da suka kamata saboda gujewa toshe magudanar ruwa don gujewa ambaliyar ruwa.

Ya ce domin guje wa aukuwar ambaliyar ruwa gwamnati na gina hanyoyi tare da fitar da hanyoyin ruwa a jihar.

A taron hukumar KEPA ta wayar da kan daliban makarantar sakandaren na gwamnati dake Rigasa mahimmancin shuka itatuwa sannan ta Basu irin itatuwa domin su suka.

Amfanin shuka itatuwa ga muhalli

1. Tatatuwa na taimakawa wajen rage karfin iska.

2. Itatuwa na samar wa mutum tsaftacen iskan da yake shaka wato ‘Oxygen’ sannan iskan ‘carbondioxide’ da mutum ke fitar wa na taimaka wa itatuwa wajen girma.

3. Itatuwa na hana rairayar ƙasa.

4. Yana hana ambaliyar ruwa

5. Itatuwa na samar da inuwa dake nishadantar da mutum.