JIKI MAGAYI: Na hakura da tafiyar Buhari daga yau, Kwankwaso zan yi – Sirajo Sa’idu

Wani mashahurin masoyin Buhari mai suna Sirajo Sa’idu mazaunin garin Wurno jihar Sokoto ya sanar wa magoya bayan sa cewa daga yanzu bashi ba Buhari, ya hakura da tafiyar.

Sirajo mutum ne da yayi suna kuma ya shahara wajen kare shugaban Kasa a shafukan sada zumunta. Ko a cikin wannan mako ya rubuta cewa ” Idan na ga hoton Buhari, sai in ji zuciyata ta yi haske, farinciki ya dabaibaye ni saboda tsananin so” amma kuma yanzu ya ce bashi ba Buhari.

” Abinda ya sa na yi haka kuwa shine mahara sun sace yan uwa na su biyar. Na rubuta a shafin Facebook dina amma babu wani da ya kawo min dauki. Haka aka barni da karo-karo muka tara kudin fansa har kuma karbo su daga mahara.

” Babu amfanin ci gaba da nuna soyayya ta ga Buhari wanda bai damu da mu ba. Kwankwasiyya zan yi daga yanzu.

Sai dai kuma masu bin sa a Facebook sun rika gwasale shi, suna yi masa dariya. Wasu na cewa sai yanzu ya sanda haka da dai sauransu.