RANAR WANKE HANNAYE: Wanke hannaye na samar da kariya daga cututtuka akalla kashi 50 cikin 100

Karamar ministan muhalli Sharon Ikeazor ta yi kira ga mutane da su rika wanke hannay su da ruwa da sabulu cewa yin haka na samar da kashi 50% na kariya daga kamuwa da cututtuka sannan da kashi 25% daga cututtukan dake kawo sirkewar numfashi.

Sharon ta fadi haka ne a taron ranar wanke hannu ta duniya da aka yi a Abuja.

Ta ce taron bana ya fi mai da hankali ne wajen ganin mutane sun ɗauki darasi da yadda annobar Korona ya yi wa mutanen duniya.

Sharon ta ce mutane da dama a Najeriya basu damu da su rika wanke hannaye da ruwa da sabulu ba sai dai ruwa kawai domin a ganin su sabulu na wanka ne da wanki.

Bincike ya nuna cewa kashi 40% na mutanen duniya na fama da karancin ruwa da sabulun wanke hannaye.

“A dalilin haka ya sa yara musamman ‘yan ƙasa da shekaru biyar ke kamuwa da cututtuka da dama wanda akarshe ma su bar duniya.

Yara sama da miliyan 3.5 na fama da cutar amai da gudawa a duniya kuma an gano cewa rashin wayar musu da kai ne ke kai su ga afkawa cikin wannan matsalar.

“Ya kamata idan an yi tari a wanke hannaye da ruwa da sabulu, kafin a ci abinci da bayan an ci abinci a wanke hannaye da ruwa da sabulu.

“Idan an yi amfani da bandaki ko an wanke wa yaro bahaya a wanke hannu da sabulu kafin a taba abinci.

A taron bana ma’aikatar muhalli tare da ma’aikatar ilimi sun gudanar da gasar amsa tambayoyi a wasu zababbun makarantun firamare shida a Abuja domin wayar wa yara kai sanin mahimmancin tsaftace muhallin su da jikinsu domin samun kariya daga kamuwa daga cututtuka.

Makarantar da ta yi nasara sun samu kyautar wurin wanke hannaye da sabulai.