Ko kotu ta raba auren magidancin da yayi barazanar kashe kan sa idan ba a raba shi da matar sa ba

Wani magidanci mai suna Amos Akinlolu mai shekara 64 ya shigar da kara a kotun gargajiya dake Mapo a Ibadan domin kotun ta raba aurensa da ya kusa shekara 30 da matarsa Funmilayo.
Akinlolu ya ce yana bukatar kotu ta raba wannan aure saboda yadda matarsa ke fasikanci rana tsaka yana ji yana gani bababu abinda ya dame ta
“Tun da na gano cewa Funmilayo na mu’amala da maza a waje zaman lafiya ya kare a gidana. Na gaji da auren Funmilayo saboda bin mazan da take yi a ganina barazana ce ga rayuwata.
“Idan har kotu bata raba auren mu ba zan kashe kai na domin ni a ganina shine kwanciyar hankalina.
Sai dai kuma Funmilayo ta karyata korafi da zargin da mijin ta yake yi a gaban alkali.
Ta ce tun da suka yi aure Akinlolu bai taba kamata da wani tana lalata da shi ba.
Ya’yan ma’auratan su biyar sun ta ya mahaifin su, rokon kotu a raba auren don a samu zaman lafiya.
A dalilin haka alkalin kotun Mrs Imoleayo Akinrodoye ta warware kullin auren.
Akinrodoye ta ce ‘ya’ya uku cikin biyar din da ma’auratan suka haifa za su ci gaba da zama da mahaifiyar su saboda karancin shekaru.
Ta kuma ce Akinlolu zai ba Funmilayo Naira 30,000 kudin da za ta biya hayar gidan zama.
Sannan ya biya naira 10,000 kudin alawus din kwasan kayan ta daga gidan sa.
Daga nan Kuma duk wata zai rika aika mata da naira 30,000 kudin ciyar da ‘ya’yan sa uku dake tare da ita.