PANDORA PAPERS: Yadda Gwamna Abiodun na Ogun ya nunke Gwamnatin Najeriya baibai

An bankaɗo yadda Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun ya nunke Gwamnatin Tarayya baibai, ya kafa kamfanonin karkatar da kuɗaɗe a ƙasashen waje guda biyu.

Binciken da PREMIUM TIMES da gamayyar takwarorin ta su ka yi, an tabbatar da Abiodun ne mamallakin wasu kamfanoni biyu da ke Tsibirin British Virgin Islands.

Ƙarin bincike ya tabbatar cewa Abiodun bai lissafa da kamfanonin ba a lokacin bayyana kadarorin sa ga Hukumar Tantance Kadarorin Ma’aikata (CCB).

Takardun bayanan da PREMIUM TIMES ta bi diddigi sun nuna Gwamna Abiodun shi ne uwa kuma shi ne uba na kamfanin Msrlowes Trading Corporation, a British Virgin Islands.

Sannan kuma shi ne mai kamfanin Heyden Petroleum Limited, kamfanin da shi ma Abiodun bai lissafa shi a cikin kadarorin da ya mallaka ba, kafin ya zama gwamna.

Abiodun ya ɗauki hayar wani kamfanin Dubai mai suna SFM Corporate Services, inda su ka ba shi shawarar yadda zai kafa kamfanin da zai buɗe wa asusun banki a waje, ya na damfara kuɗaɗe.

Daga nan sai SFM Corporate ya ɗauki sojan-hayar Aleman, Cordero, Galindo & Lee (alcogal) na ƙasar Panama, domin yi wa kamfanin Marlowes Trading Corporation na Abiodun.

An yi masa rajista a Tsibirin British Virgin islands a ranar 12 Ga Janairu, 2015, kamar yadda PREMIUM TIMES ta ga takardun rajistar kamfanonin.

Daga nan sai Abiodun ya raba hannayen jari ga “Adedapo Oluseun Abiodun’.

Ba a san irin hada-hada, harƙalla ko daƙa-daƙar da ake yi cikin kamfanin Morlowes ba. Amma dai kamfanin ya ci gaba da hada-hada, ba daga Ofishin SFM Corporate Services da ke Dubai, a lamba H Dubai-Office Building, kan titin Sheikh Zayed.

PREMIUM TIMES ta gano cewa wani mai suna Samuel Kim Oh.

Dapo Abiodun ke da kamfanin Heyden Petroleum Limited a Najeriya, kuma shi ne ke da na ƙasar waje, inda ya ke kauce wa biyan haraji a Najeriya.

An kafa reshen Heyden Petroleum Limited a Najeriya a cikin 2001.

Wata wasiƙa da aka rubuta ranar 21 Ga Maris, 2016 ta nuna Abiodun ne mamallakin Heyden Petroleum Limited na Tsibirin BVI.

A cikin wasiƙar, Abiodun ya sanar da SFM cewa ya na so a damƙa ikon kula da kamfanin ga wani mai suna Chikezie Nzelum. Amma ayyukan ofis da ma’aikata kawai zai kula. Banda harkar hada-hadar kuɗaɗe.

PREMIUM TIMES ta tabbatar Abiodun bai saka sunayen kamfanonin biyu a cikin kadarorin sa ba, a lokacin da ya zama gwamna cikin 2019.

Hakan kuwa ya karya sharaɗi da ƙa’idoji da dokokin Najeriya.

Sashe na 11 na Dokar Najeriya ya gindaya cewa duk wanda gwamnati ba bai wa muƙami, to ya hanzarta bayyana kadarorin sa a cikin wata uku na farkon hawan sa mulki. Kuma ya cire hannun sa daga cikin kamfanin.

PREMIUM TIMES ta kuma gano cewa Abiodun ya na ɓoye kuɗaɗe a wani bankin Switzerland da ke Zurich, mai suna UBS.

PREMIUM TIMES ta yi ta aika wa Gwamna Abiodun saƙon neman ƙarin bayani, amma bai maida amsa ba.

Shi ma Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna, wato Kunle Somorin, an sha aika masa saƙonnin, amma bai maido amsa ba.

Sai dai wani makusancin gwamnan ya shaida wa wakilin mu cewa Gwamna Abiodun mutumin kirki ne, ba ɗan gada-gada ba ne. “Mai yiwuwa manta ya yi bai bayyana kamfanonin a cikin kadarorin sa ba.”