RANAR CUTAR HEPATITIS: Cutar na yaduwa kamar wutan Daji duk da akwai wadatuwar rigakafin ta

Cutar Hepatitis cuta ce dake kama huhu inda rashin gaggauta neman magani da wuri zai iya sa cutar ta rikiɗe ta zama dajin dake kama huhu.

Cutar na da nau’uka biyar da suka hada da Hepatitis A,B,C,D da E. Jami’an lafiya sun ce nau’ukan B da C ne suka fi yaduwa da hallaka mutane a duniya.

Jami’ar asibitin koyarwa dake jihar Legas Kuma kwararriya kan cutar Hepatitis Emuobor Odeghe ta ce ba a warkewa daga cutar amma akwai maganin da ake badawa domin hana kwayoyin cutar cigaba da yaduwa a jikin mutum.

Odeghe ta ce mafi yawan lokuta akan gano alamun cutar a jikin mutum bayan cutar ya gama illata huhum mutum amma rashin iya cin abinci, amai, zazzabi, canjin kalan fitsari zuwa baki, canjin kalan ido zuwa ruwan kwai da yawan ciwon ciki.

Yaduwar cutar a duniya

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa a shekarar 2019 akalla mutum miliyan 296 na dauke da cutar Hepatitis B sannan duk shekara ana samun mutum miliyan 1.5 dake kara kamuwa da cutar a duniya.

WHO ta ce Hepatitis B da ke rikida ya zama cutar dajin dake kama huhu ya yi ajalin mutum 820,000 a shekarar 2019.

A Najeriya dake da akalla mutum miliyan 200 na da kashi 8.1% na mutanen dake dauke da Hepatitis B da kashi 1.1% na mutanen dake fama da Hepatitis C a duniya.

Zuwa yanzu mutum sama da biliyan biyu sun kamu da Hepatitis B a duniya sannan a Afrika mutum miliyan 90.

Wani jami’in lafiya dake aiki da asibitin FMC Gusau jihar Zamfara Bashir Gusau ya ce yaduwar cutar ya zama ruwan dare dake bukatan a dauki matakan dakile yaduwar ta cikin gaggawa.

Dalilin da ya sa cutar ke yaduwa

1. Rashin Sani

Rashin sani na daga cikin dalilan da ya sa mutane da dama ke kamuwa da cutar ba tare da sun sani ba.

Sakamakon binciken ya nuna cewa cutar zai iya cutar da hukun mutum idan kwayoyin cutar sun yi sama da makonnin shida a jikin mutum. Bayan haka ne cutar ke nuna alamu a jikin mutum.

2. Rashin yin gwajin cutar

Rashin zuwa asibiti domin duba lafiya na daga cikin matsalolin da mutane da dama ke fama da shi.

Sakamakon binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar game da yin gwajin cutar ya nuna cewa asibitoci da dama na gudanar da gwajin sai dai tsada.

Rashin yin gwajin cutar na hana mutane sanin matsayinsu game da cutar wanda hakan ke sa ake gano cutar a kurarranen lokaci.

3. Allurar rigakafin cutar

Asibitoci da dama na yi wa mutane allurar rigakafin cutar sai dai matsalar shine yara kanana ne kadai ake yi wa rigakafin kyauta.

Bisa ga tsari kamata yayi babba ko yaro ya yi allurar rigakafin Hepatitis sau uku domin samun kariya daga kamuwa da cutar.

Gwamnati ta saka yin allurar rigakafin Hepatitis cikin jerin alluran rigakafin da ya kamata yara na yi kyauta domin inganta lafiyar su amma manya na biyan Naira 2,000 wa kowani allurar daya sannan wa allurar uku da ya kamata su yi naira 6,000.

Jami’an lafiya sun ce samar wa mutane lafiya ta gari a farashi mai sauki zai taimaka wajen rage yaduwar cutar.