Yadda mata ta da mahaifiyar ta suka talauta ni karkaf ta hanyar tsula kudin cefane – Magidanci a kotu

A kotu dake Mapo ne wani magidanci kuma ma’aikacin banki mai suna Biliameen Oyesola ya roki kotun da raba aurensa na shekara shida saboda yadda matarsa Rofiat ke damfaran sa kudin cefane.
Oyesola ya ce matarsa kan yi yaji ta koma gidan mahaifiyarta a duk ranar da ta damfare shi.
“Kullum ina bada kudin cefane masu kauri, bayan sun kitsa yadda za su cucen i da mahaifiyarta.
“Tun da na fahimci haka ne na ke tilasta ta ta ta nuna min takardar shaidar siyan kaya amma Rofiat ta ki nuna wa.
“Rofiat da mahaifiyarta sun yi kaurin suna a harkar da suke yi inda bayan ta haifi dana na biyu da ita da mahaifiyarta suka kara kudaden maganin da likita ya bada a siya.
“A wannan ma na ce a nuna mun takardan shaida amma suka ki.
Bayan haka Oyesola ya ce haka kawai Rofiat take yin yaji zuwa gidan su ba tare da mun yi fada ko ta yi min laifi ba.
“Mutane da dama musamman limamin masallacin dake kusa da gidan mu sun yi mata fada amma bata canza hali ba.
“Burin Rofiat da mahaifiyarta shine su mallake ni.
“Rofiat da mahaifiyarta sun hana ni jin dadin aure na sannan sun hana ni karo mata.
Ya roki kotun da ta ba shi ikon kula da ‘ya’yan su biyu.
Alkalin kotun Mrs S.M. Akintayo ta dage shari’a zuwa ranar 10 ga watan Agusta domin Rofiat ta samu halartar kotun.