RA’AYIN PREMIUM TIMES: Rashin cancantar yi wa ‘Yan Majalisa watandar mahaukatan kuɗaɗe, lokacin raɗaɗin tsadar rayuwa

Yayin da talakawan Najeriya ke cikin halin raɗaɗin tsadar rayuwar da rashin kyakkyawan shugabanci ya haddasa masu, su kuwa ‘Yan Majalisa sun nuna babu ruwan su da mawuyacin halin da al’ummar da su ka zaɓe su ke ciki.
Abin da kawai ke gaban su shi ne yadda za su yi rayuwar jin daɗi su da iyalan su a Abuja, a wannan lokacin da kowa ya shiga taitayin sa, saboda raɗaɗin ƙuncin rayuwa.
Ƙiri-ƙiri ko kunyar talakawa ba su ji, sun ware wa kan su jimillar Naira biliyan 110, don sayen kayayyakin more jin daɗin rayuwa a Abuja. Sauran talakawa da marasa galihu kuma sama da miliyan 100 an bar masu Naira biliyan 500. Kuma a cikin su ko mutum goma ba zai amfana da tallafin ba.
Za a sai wa ‘yan majalisa zunduma-zunduman motoci masu sulken hana harsashi ratsawa cikin motar. Su kuma talakawa an bar su a hannun ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda su na kisa, ba ƙaƙƙautawa.
‘Yan Majalisar Tarayya sun ajiye rigar kunya a gefe, sun nemi a yi masu ƙarin albashi da alawus-alawus, saboda wai rayuwa ta yi tsada a yanzu.
Amma kuma har yanzu ana ta kwan-gaba-kwan-baya kan batun ƙara wa ma’aikata albashi.
Saboda haka wannan rashin mutunci da rashin tausayin talakawa ne a ce masu wakiltar marasa galihu su riƙa kamfatar mahaukatan kuɗaɗe don su ji daɗin rayuwar su, musamman a lokacin da talakawa ke cikin tsananin tsadar rayuwa.
Hakan da su ka yi ya nuna cewa tun ba a je ko’ina ba, ba kishin jama’ar da ya zaɓe su ne a gaban su ba. Hakan da su ka yi ya daɗa janyo masu baƙin jini da tsana daga cikin talakawa.
Jama’a ku dubi yadda wasu ‘yan majalisar da su ka sauka su ka sace komai daga ofishin su. Hatta talabijin da darduma ba su bari ba. Wannan abin kunya ce tabbas. Kuma abin takaici har yau babu wani hoɓɓasan da aka yi domin a dawo da kayan. Tir, girma dai ya faɗi.
Ko ma dai me za a ce, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya fara saƙa da mugun zare.
Sabon salon tsarin mulkin Shugaba Bola Tinubu a cikin wata biyu kacal ya gigita ‘yan Najeriya. Cire tallafin fetur da sakin Naira a cikin kasuwa ba tare da makiyayi ba, ya haifar da tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci zuwa kashi 22.7%.
Rabon da a fuskanci irin wannan balbalin tsadar farashin kayan masarufi da na abinci kuwa, tun cikin 2005.
Kuɗin zirga-zirga a motocin sufuri ya ƙaru. Mutane da dama sun gwammace su riƙa tafiya a ƙasa. Wasu sun ajiye aiki, saboda albashin su ba zai iya biyan kuɗin motar da su ke kashewa zuwa ofis ba.
Abinci ya yi tsada a birane da ƙauyuka. Cefane ya gagari magidanta da dama, saboda ɗan abin da su ke samu ba ya isar su. Waɗanda ambaliyar ruwa ta janyo wa mummunar asara tun 2022, har yau gwamnatin tarayya ba ta cika alƙawarin da ta masu ba.
Karatu a makarantun jami’o’in ƙasar nan na neman ya gagari ‘ya’yan talakawa, domin a wasu makarantun ƙarin kuɗin makaranta ga ɗalibai ya kai Naira 256,000.
Sai ga shi duk da irin wannan mawuyacin hali da ake ciki, su kuma ‘yan majalisa hankalin su ya fi karkata ga abin da za su samu su ji daɗin more rayuwar su.
Don haka shawarar da za mu bai wa ‘yan majalisa ita ce su kwaikwayi na wata ƙasa, ko wasu ƙasashen da kwata-kwata ba su ma kama ƙafar da za a kwatanta ƙarfin tattalin arzikin su da na Najeriya ba.
Sannan kuma kada Shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa Yusuf Abbas kada ya ƙara yawan kwamitocin majalisa daga 110 da ya taras, zuwa 134 da ya ke son kafawa.
‘Yan Najeriya fa sun gaji da wannan bulkara da ragabzar kuɗaɗe da ake yi a kan idon su. Ido ai mudu ne. Idan bai san kunya ba, to ya san kima.