DIPHTHERIA: Akwai yara da dama da ba a yi musu allurar rigakafin cutar ba – NPHCDA

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa NPHCDA Faisal Shuaib ya bayyana cewa har yanzu akwai yara da dama da ba a yi musu allurar rigakafin cutar Diphtheria ba.

Shuaib ya fadi haka ne a taron dakile yaduwar cutar da aka yi a Abuja.

Shuaib ya ce rashin yin allurar rigakafin cutar ka iya dawo da hannun agogo baya na kokarin dakile yaduwar cutar da gwamnati ke yi.

Yin allurar rigakafi

Shuaib ya ce hukumar za ta hada hannu da gwamnatocin jihohin da cutar ta bayyana domin a yi wa mutane rigakafin.

Ya ce hukumar za ta rika amfani da magungunan ‘pentavalent, tetanus da diphtheria’ wajen yin rigakafin.

Bayan haka ya ce an raba yadda za a yi aikin zuwa rukuni rukuni ta yadda zai kai ga ko ina a fadin kasar nan tun daga jihohi har zuwa kananan hukumomi.

Cutar Diphtheria

Daga watan Mayu 2022 zuwa Yuli 2023 an samu mutum 2,455 da ake zargin sun kamu da cutar a jihohi 26.

Daga ranar 27 ga Yuli 2023 an samu mutum 836 da suka kamu da cutar a kananan hukumomi 33 dake jihohi 8 da Babban Birnin Tarayya Abuja da suka hada da Cross River, Kano, Katsina, Kaduna, Legas, Osun da Yobe.

Zuwa ya zu cutar ta Yi ajalin mutum 83 inda hakan ya zama dole a Yi wa mutane musamman yara kanana allurar rigakafin cutar.

Ga abubuwa 9 game da cutar Diphtheria

1. Menene cutar Diphtheria

Cutar Diphtheria cuta ce da kwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ ke haddasa wa.

Babu babba ko yaro a yadda Cutar ke yaduwa amma jami’an lafiya sun ce cutar ya fi kama yara kananan musamman wadanda ba su yi allurar rigakafin cutar ba.

2. Hanyoyin kamuwa da cutar.

Ana iya kamuwa da cutar ta hanyar sumba musamman idan ana yin sumban da mutane daban-daban.

Cutar na yaduwa idan ana yawan zama kusa da masu fama da cutar.

Idan mai dauke da cutar ya yi tari ko atishawa ba tare da ya rufe bakinsa ba.

Sannan da yawan yin amfani da kayan da masu fama da cutar suka yi amfani da su kamar chokali, Kofi, hakichin da sauran su.

3. Mutanen da suka fi kamuwa da cutar

Cutar Diphtheria ya fi kama yara da manya musamman wadanda tun farko ba su Yi allurar rigakafin cutar suna yara ba sannan da kin yin allurar rigakafin yayin da suka girman.

4. Alamun cutar

Akan gane alamun cutar bayan ranar farko zuwa rana ta 10 bayan kamuwa da cutar.

Alamun cutar sun hada da zazzabi, yoyon hanci, ciwon makogwaron, idanun za su Yi jajawur, tari da Kumburin wuya.

Wasu lokuta mai fama da cutar zai rika ganin wasu farin abubuwa na fitowa da a kusa da makogwaron sa wanda ke hana mutum iya yin numfashi da hadiyan abinci.

5. Abin da ke haddasa cutar

Kwayoyin cutar ‘Corynebacterium diphtheria’ ne ke haddasa cutar inda yakan kama hanci, makogwaron da fatara mutum.

Rashin tsaftace muhalli na haddasa cutar.

6. Ire-iren cutar Diphtheria

Cutar diphtheria ya rabu biyu inda akwai ‘Classic respiratory’ wanda kan kama hanci makogwaro sannan da ‘Cutaneous’ wanda kan kama fatar mutum.

7. Hanyoyin gane cutar a jikin mutum

Jami’an asibiti na iya gano cutar daga alamun kamuwa da cutar da suka fara nunawa a jikin mutum kokuma idan aka Yi wa mutum gwajin cutar.

8. Maganin cutar

Wanda ya kamu da cutar zai killace kansa sannan maganin ‘Antibiotices’ na kawar da cutar daga jikin mutum.

Sannan ruwan dumi akai-akai na taimakawa wajen rage zafi da Kumburin makogwaro.

Hanyoyin da za a kiyaye don gujewa kamuwa da cutar

A. Yin allurar rigakafi.

B. Saka takunkumin fuska musamman idan za a shiga cikin mutane.

C. Kare baki da hanci idan za a yi tari ko atishwa.

D. Tsaftace muhalli, wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.

E. Zuwa asibiti da zaran an kamu da zazzabi ko idan ba a gane lafiyar jiki ba.