Matawalle, Bagudu, Lalong, sun shiga cikin sabbin sunayen ministoci 19 da Tinubu a mika wa Majalisa

A yau Laraba shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sabbin jerin sunayen ministoci 19 ga majalisar dattawa domin tantancewa.
Daga cikin wadanda aka mika sunayen su akwai tsohon gwamnan jihar Osun, Adegboyega Gboyega; tsohon gwamnan Kebbi Atiku Bagudu; tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle; tsohon gwamnan Yobe, Ibrahim Geidam; tsohon gwamnan Filato, Simon Lalong; tsohon sanata daga jihar Bayelsa, Heineken Lokpobiri da Shuiabu Abubakar Audu.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya bayyana sunayen a zauren majalisar bayan kammala tantance sunayen ministoci 28 da aka aika majalisar.
Da wannan sabon jerin sunayen, adadin wadanda aka tura sunayen su majalisara dattawa yanzu ya zama 47.
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ne ya mika sunayen ga shugaban majalisar dattawan a yayin da majalisar ke aikin tantyance wadanda aka mika sunayen su.
Shugaban majalisar dattawan ya ce majalisar za ta zauna ranar Juma’a domin fara tantance sabbin ministocin da aka turo sunayen su.