RAƊAƊIN CIRE TALLAFIN FETUR: ‘Yanzu ƙaramin albashin Naira 30,000 ko tankin Keke NAPEP ba zai cika ba’ – Shugaban NLC

Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin NLC da TUC na Jihar ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya shammaci ‘yan Najeriya, ya cire tallafin fetur ana tsakiyar murnar rantsar da shi.
Ya ce tun daga lokacin ya ƙara tsunduma ‘yan Najeriya cikin raɗaɗi da ƙuncin tsadar rayuwa.
Shugaban na Jihar Enugu ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin zanga-zangar game-gari da aka karaɗe ƙasar da ita, domin nuna wa sabuwar gwamnatin Tinubu irin matsanan halin ƙuncin da ake ciki a faɗin nan.
Da ya ke magana dangane da cire tallafin fetur ba zato ba tsammani, Fabian Nwigbo na NLC da takwaran sa na TUC Ben Asogwa, sun ja zugar masu zanga-zanga har Gidan Gwamnatin Enugu, inda Mataimakin Gwamna, Ifeanyi Ossai da wasu jami’an gwamnati.
Sun ce sun je Gidan Domin su isar da saƙon su ga Shugaba Bola Tinubu, ta hannun Gwamna Peter Mbah.
“Shugaba Bola Tinubu ya shammaci ‘yan Najeriya, yayin da ya janye tallafin ana cikin rantsar da shi, lokacin da aka shagala cikin murnar hawan sa mulki.
“Ya cire tallafin fetur, amma har yanzu ba a ƙara wa ma’aikata albashi ba. Yanzu ƙaramin albashi na Naira 30,000, ko tankin Keke NAPEP ba zai iya cikawa ba.”
A Abuja kuwa, NLC da TUC sun ce laƙanin Naira 8,000 ga marasa galihu cin fuska da raina talakawa ne.
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa NLC, ta bayyana cewa raba wa talakawa tallafin Naira 8,000 a mawuyacin halin da aka jefa ‘yan Najeriya a ciki, “cin fuska ne da raina masu wayau.”
Shugaban NLC na Ƙasa, Joe Ajaero ne ya bayyana haka a ranar Laraba, a cikin saƙon da ya aika wa ma’aikata, a Abuja, lokacin da ya ke jawabi a wurin zanga-zanga.
“Raba wa talakawa marasa galihu Naira 8,000 a wannan halin cin fuska ne a gare su, kuma an raina masu wayo. Mu na kira ga Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da muka yi da ita, wadda idan aka yi aiki da ita za ta zama alfanu ga talakawa a faɗin ƙasar nan.”
Bayan cire tallafin fetur, gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta fito da wasu tsare-tsaren sauƙaƙa ƙuncin rayuwa ga talakawan ƙasar nan da ma’aikatan gwamnati masu ƙaramin ƙarfi.
Sai dai kuma akasarin masu bayyana ra’ayin su na ganin cewa duk da tallafin ya yi kaɗan, to ba zai kai ga waɗanda su ka fi cancanta su ci moriyar sa ba.
Sannan kuma a sama da talakawa miliyan 100, za a bayar da tallafin ne ga mutum miliyan 12 kaɗai.
Sannan kuma wani bayani da Wale Edun ya yi a lokacin tantance shi minista, ya ƙara sa guyawun talakawa sun yi sanyi.
Edun cewa ya yi duk zafin talaucin mutum, ba za a ba shi tallafin na Naira 8,000 ba, sai ya na da asusun ajiyar kuɗaɗe a bankuna.
“Maganar tallafin nan duk shafa-labari-shuni ce. Har an shiga wata na uku kenan da cire tallafin fetur, amma ba a bayar da tallafin ko sisi ba. Babu wani ma’aikacin da ya samu tallafin Naira 1 tal daga gwamnati. Kuma har yanzu babu ma alamar motocin da aka ce za su samar da sassaucin kuɗaɗen zirga-zirgar ko guda ɗaya.” Haka Ajaero ya ja jaddada.
Ya ce kada Shugaba Tinubu ya shiga sahun shugabanni masu cika mutane da nuna damuwar su kan matsaloli kaɗai.
“Ya kamata Shugaban Ƙasa ya tashi tsaye ya sa a kamo manyan ɓarayin gwamnati da suka sace mana kuɗaɗe, su dawo da su.”
Haka shugaban na NLC ya bayyana a fusace.
Ya ce bayan wannan zanga-zangar, za su je su yi nazarin abin da zai biyo baya. Wannan inji shi zai bayar da ƙofar tafiya yajin aiki, idan gwamnati ba ta yi komai a kai ba.